An kuma: OAU ta kama malami da laifin lalata da daliba, ta mika shi hannun 'yan sanda
Hukumomin jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun sun dakatar wani malami mai suna Monday Omo-Etan a kan zarginsa da ake da lalata wata daliba mai shekaru 19.
Kamar yadda mai magana da yawun jami'ar, Abiodun Olarewaju ya sanar, jami'ar ta mika Omo-Etan zuwa hannun 'yan sanda.
Kamar yadda takardar da makarantar ta fitar ta ce, "Ba a kai makonni uku ba da jami'ar Obafemi Awolowo ta bayyana rashin amincewarta da cin zarafin dalibai, ta bincika tare da korar wani malami mai suna Olabisi Olaleye, sai ga wata matsalar ta kara kunno kai."
DUBA WANNAN: Katsina: Matar aure mai shekaru 17 da caka wa mijinta wuka ya mutu saboda cajar waya
Takardar ta kara da cewa, "hukumar ta dakatar da Omo-Etan, malami a makarantar a kan cin zarafi da kuma lalata da wata daliba mace mai shekaru 19."
"Hukumar makarantar na kara jaddada cewa ba za tayi kasa a guiwa ba kuma ba za ta gaji ba har sai ta kakkabe matsalar cin zarafi da lalata da dalibai a makarantar," takardar ta kara da cewa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng