Jami'ar Legas ta dakatar da wani malami akan zargin lalata da dalibai mata

Jami'ar Legas ta dakatar da wani malami akan zargin lalata da dalibai mata

- Hukumar jami'ar jihar Legas ta kara dakatar da wani malaminta

- A binciken sirri da BBC tayi na malaman jami'a masu lalata da dalibai, ta nado harda Oladipo

- Mataimakin shugaban bangaren sadarwa na jami'ar ne ya sanar da cigaban a jiya ranar 8 ga watan Oktoba

Jami'ar jihar Legas ta dakatar da wani malami mai suna Dr Samuel Oladipo na bangaren karatun tattalin arziki na makarantar bayan da aka hango shi a bidiyon bayanan da BBC ta binciko na malaman jami'o'i masu lalata da dalibai.

An ga Oladipo a faifan yana takura 'yar jarida Kiki Mordi, wacce ta yi basaja a matsayin daliba, don lalata da ita.

KU KARANTA: Hotunan bikin wata kyakyawar gurguwa da angonta sun jawo cece-kuce a arewa

A faifan bidiyon, an ga Oladipo na bukatar Kiki da ta bashi lokaci su hadu har da zolayarta akan manyan nonuwanta. Oladipo bai tsaya nan ba, ya kai Kiki inda ake kira "Cold room" a jami'ar; guri ne da malaman jami'ar ke kai dalibai mata don baje kolinsu da watayawa.

Mataimakin shugaban bangaren sadarwa na jami'ar, Taiwo Oloyede, wanda ya bayyanawa jama'a dakatar da Oladipo, ya ce hukumar jami'ar ta yanke hukuncin hakan ne a ranar Talata, 8 ga watan Oktoba.

A ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba, jami'ar ta dakatar da malaminta, Dr Boniface Igbeneghu bayan da 'yar jarida Kiki Mordi ta nado maganganu da aiyukansa na neman lalata da ita yayin da ta je masa a matsayin 'yar shekaru 17, da bukatar taimakonsa don samun gurbin karatu a jami'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel