Bincike: Kashi 63 na daliban jami'a ana lalata da su saboda shigar banzar da suke yi

Bincike: Kashi 63 na daliban jami'a ana lalata da su saboda shigar banzar da suke yi

- A wani sabon bincike da aka yi a manyan makarantu da ke Legas, an gano cewa shigar banza ce a kan gaba wajen sa malamai su nemi dalibai

- A binciken, an gano cewa akwai kungiyoyin asiri, shan miyagun kwayoyi da sauran abubuwa da ke kawo matsalar fyade

- Wasu daliban sun bayyana cewa, ba mata kadai ke fuskantar kalubalen cin zarafi ba, har da dalibai maza

A wani sabon kididdiga da kiyasi da aka yi a manyan makarantun da ke jihar Legas, ya bayyana cewa shigar banza ce ke kawo matsalolin fyade da kuma lalata da malamai ke yi da daliban.

Kamar yadda binciken wanda Africa Polling Institute (API) da kuma Heart Minders Advancement Initiative suka bayyana a ranar Talata, kashi 63 na dalibai sun zabi shigar banza a matsayin silar fyade da kuma lalata da dalibai.

Wasu kashi 36 kuwa sun danganta hakan da miyagun kwayoyi, kashi 12 daga ciki sun ce rashin iya danne sha'awa ne. Wasu kashi 5 sun danganta hakan da laifin shan barasa.

Sauran abubuwan da ke kawo hakan sun hada da kungiyoyin asiri, rashin tsaro da rashin da'a daga dalibai da malamai.

Kiyasin API, kamar yadda manema labarai suka bayyana, ya bi manyan makarantu a Legas guda shida da suka hada da jami'ar jihar Legas, kwalejin kimiyya ta Yaba, foliteknik din jihar Legas, kwalejin Ilimi ta Akoka da kwalejin ilimi ta Ijanikin. An samu wadanda suka amsa tambayoyin har sun kai mutane 1,642 masu shekaru 18 zuwa sama. An tattauna dasu ne a watan Augusta.

"Wannan binciken ya jaddada binciken BBC wanda ta yi a kan malamai masu lalata da dalibai. An yi binciken ne a manyan makarantun Najeriya da Ghana tare da kasashen Afirka ta Kudu don duba kalubalen da daliban manyan makarantun ke fuskanta," in ji takardar.

KU KARANTA: Abubuwa 7 da suka faru a shekarar 2019 wadanda suka kawo kace-nace a Najeriya

"Zargin lalata da dalibai a manyan makarantun Najeriya ya zama babban kalubale a halin yanzu. An gano cewa, hukumomin makarantun na kokari kadan ne wajen shawo kan wadannan matsalolin.

"A kuma wani rahoto, daliban da suka kai kara a kan wannan mummunan lamarin kan fada halin tsangwama daga malamai ko kuma hukumomin manyan makarantun."

"Kashi 61 na daliban sun tabbatar da sun san ana lalata da dalibai, kashi 79 kuwa sun tabbatar da cewa mata ne ake bibiya. Kashi 14 daga ciki kuwa sun tabbatar da cewa, malamai mata na bibiyar dalibai, ba mazan bane kadai ke shiga wannan halin ba," takardar ta kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel