Jirgin Sama Dauke da Manyan Mutane Daga Abuja Ya Ci Karo da Cikas, Ya Fantsama Daji
- Mutane da dama sun shiga fargaba yayin da wani jirgin sama ya kauce hanya a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya
- Jirgin saman wanda mallakin kamfani Dana Air ne ya gamu da matsalar a yau Talata 23 ga watan Afrilu a jihar
- Jirgin wanda ya sauko fasinjoji 83 ya taso ne daga birnin Abuja zuwa jihar Legas kafin cin karo da matsalar sanadin ruwan sama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - An shiga fargaba yayin da jirgin sama ya kauce hanya a jihar Legas bayan kwaso fasinjoji daga Abuja.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 23 ga watan Afrilu a jihar yayin da jirgin ya yi saukar gaggawa tare da kauce hanya.
Yaushe jirgin ya kauce hanya a Legas?
Channels TV ta tattaro cewa lamarin ya rutsa ne da jirgin saman kamfanin 'Dana Air' wanda ya taho daga Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a samu karin bayani ba, sai dai an tabbatar da cewa babu rasa rai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne saboda dalilin ruwan sama da aka tafka da safiyar yau.
An tabbtar jirgin saman ya na dauke da fasinjoji akalla 83 daga birnin Abuja zuwa Legas.
A wani faifan bidiyo da Aminiya ta wallafa an gano fasinjojin suna fitowa daga jirgin cikin firgici bayan faruwar lamarin.
Martanin jirgin 'Dana Air' kan lamarin
Sakataren yada labaran kamfanin, Kingsley Ezenwa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce babu rauni kan matsalar da jirgin ya samu.
Ya ba fasinjojin tabbacin ci gaba da ba su kulawa na musamman inda ya ce ana kan binciken game da matsalar da ta faru.
Jirgin sama ya yi saukar gaggawa a Oyo
A wani labarin, kun ji cewa jama'a sun shiga tashin hankali bayan jirgin sama ya yi saukar gaggawa a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.
Jirgin da ke dauke da manyan mutane guda goma ya yi saukar gaggawa tare da fantsama cikin daji a jihar.
Lamarin ya faru ne a ranar 26 daga watan Janairun shekarar 2024 da misalin karfe 11:00 a jihar.
Asali: Legit.ng