Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma A Najeriya

Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma A Najeriya

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Mista Frank Esiwo Ozue, mataimakin karamar hukumar Isoko ta Arewa, Jihar Delta
  • Wani cikin yan uwansa ya tabbatar da afkuwar lamarin yana mai cewa maharan sun bar motarsa da wayarsa ta salula a kan titi inda suka tare shi
  • DSP Bright Edafe, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Delta, ya ce bai riga ya samu cikakken bayani kan sace Ozue ba amma za su yi duk yiwuwa don ceto shi

Jihar Delta - Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban karamar hukumar Isoko ta Arewa, Frank Esiwo Ozue kamar yadda The Nation ta rahoto.

An gano cewa an sace Ozue ne a ranar Lahadi a garin Ogor da ke karamar hukumar Ughelli ta Arewa na Jihar Delta a hanyarsa na zuwa garin Patani.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga Sun Budewa Sanata Ubah Wuta, An Kashe Akalla Mutum 6

Taswirar Jihar Delta
Yan Bindiga Sun Sace Mataimakin Shugaban Karamar Hukuma A Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

The Nation ta tattaro cewa wanda abin ya faru da shi, shi kadai ne a lokacin da aka sace shi aka kai sh wani wurin da ba a sani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani majiya daga iyalinsa ta ce:

"Wadanda suka sace shi sun bar motarsa da wayarsa ta salula."

Majiyar ta kara da cewa yan bindigan ba su tuntubi iyalan wanda abin ya shafa ba a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Martanin yan sandan Delta

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Delta, DSP Bright Edafe ya ce bai riga ya samu cikakken bayani kan sace Ozue ba.

Amma ya bada tabbacin za a ceto shi.

Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Sarki A Wata Fitacciyar Jihar Arewa

A wani rahoton, yan bindiga a kan babura sun sake basarake a karamar hukumar Wase ta Jihar Plateau, The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hatsabibin Dan Bindiga Boderi Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Yayin Da Sojoji Suka Kashe Mataimakinsa Da Wasu

Mazauna garin sun ce an sace basaraken, Mai Martaba Dauda Mohammed Suleiman na a lokacin da yan bindiga suka kai hari fadarsa a garin Pinau, daren ranar Litinin.

Mazauni garin Wase kuma shugaban jam'iyyar Action Democratic Congress a karamar hukumar Wase, Hon. Abdullahi Gadole, ya tabbatarwa The Punch sace basaraken a Jos a ranar Talata.

Gadole ya ce tun bayan da yan bindigan suka sace basaraken zuwa wani wurin da ba a sani ba, mutanen gari sun bazama nemansa amma ba a dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel