An damke wani makiyayi dauke da bindiga kirar AK47 a jihar Enugu

An damke wani makiyayi dauke da bindiga kirar AK47 a jihar Enugu

- Jami'an Yan sanda sunyi nasarar kama wani makiyayi dauke da bindiga a jihar Enugu

- An kama makiyayin ne bayan wasu mutane sun sanar da hukumar yan sanda bayan sun ganshi

- Wanda aka kama yana tsare kuma yana taimakawa hukuma da bayyanai don zurfafa bincike

Jami'an Yan sanda a jihar Enugu sunyi nasarar cafke wani makiyayi dauke da bindiga kirar AK 47 a garin Ugbakwa a karamar hukumar Nkanu ta kudu da ke jihar. Anyi nasarar kama shi ne bayan mazauna yakin sun kai rahoto ofishin yan sanda.

Mai magana da yawun hukumar, Ebere Amaraizu tace bayan sun sami rahoton ne suka tura jami'an su zuwa unguwar inda akayi nasarar kama makiyayin dauke da bindigar ta AK 47. "Wanda aka kama din yana taimakawa Yan sanda da bayanai don cigaba da binciken su" inji Mrs Amaraizu.

An damke wani makiyayi dauke da bindiga kirar AK47 a jihar Enugu
An damke wani makiyayi dauke da bindiga kirar AK47 a jihar Enugu

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An kama mutum 7 da ake zargi da hannu cikin fashin Offa

Bayan kama makiyayi, Kwamishinan Yan sanda na jihar, Danmallam Muhammad ya ziyarci garin tare da wasu yan garin inda ya yabawa mazauna garin bisa yadda suke sa ido kan abubuwan da ke faruwa kuma suka sanar da yan sanda. Ya kara da cewa ya zama dole Yan sanda suyi aiki tare da al'umma idan ana son cin nasara.

A jawabinsa, Ciyaman din karamar hukumar Nkanu ta Gabas, Ikechukwu Ubagu, ya bayyana farin cikinsa kan yadda yan sanda suka amsa kirar cikin gagawa kuma suka kama makiyayin.

Yace a yanzu babu wani tashin hankali a garin kuma manoman suna cigaba da ayyukansu yadda suka saba. Ya kuma jadada wa Kwamishinan yan sandan cewa al'ummar garin zasu cigaba da bayar da hadin kai da hukumar.

Kwamishinan yan sandan har ila yau yayi amfani da damar don kara bawa al'umma lambobin da zasu kira don tsegunta wa yan sanda duk wani abin da basu yadda dashi ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel