Ana Tsoron Mutane Sun Ci Nama Mai Guba, Gwamnati ta Rufe Abbatuwar Dabbobi

Ana Tsoron Mutane Sun Ci Nama Mai Guba, Gwamnati ta Rufe Abbatuwar Dabbobi

  • Gwamnatin jihar Kwara ta fara bincike kan fargabar samun nama mai guba a mayankar Mandate dake babban birnin jihar, Ilorin
  • Binciken na zuwa bayan farbagar wata cuta ta kashe shanu 33, kuma ana sayar da namansu a cikin kasuwar kamar yadda aka ruwaito
  • Gwamnatin ta ce za ta rufe kasuwar domin yin feshi a mayankar kafin ci gaba da hada-hada a kasuwar da za a bude a ranar Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ilorin, Kwara-Gwamnatin Kwara ta rufe mayankar abbatuwa da ke kasuwar Mandate a na wucin gadi bisa zargin samun guba a naman dabbobin da ke mayankar.

Kara karanta wannan

Za mu hukunta masu boye kaya, Shugaban kasuwa zai yaki tashin farashin abinci

A cewar babban sakataren ma’aikatar Muhalli, Dakta Abubakar Ayinla ya ce gwamnati ta dauki matakin rufewar ne domin ta samu damar yin feshin magani da kuma tsaftace kasuwar.

Gwamnatin Kwara ta na bincike
Gwamnatin ta ce ta fara binciken akwai nama mai guba a kasuwar Mandate Hoto: UGC
Asali: UGC

Ya ce daukar matakin ya zama dole domin kare lafiyar mazauna jihar, kuma za a bude kasuwar a Laraba mai zuwa, kamar yadda The Nation ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta ce ta na binciken abatuwa

A wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin ma’aikatar lafiya da ta noma, sun ce sun dauki matakin bincike tare da magance fargabar nama mai guba a kasuwar ta Mandate.

Sanawar dauke da sa hannun kwamishinoni Dr. Amina Ahmed da Toyosi Thomas Adebayo ta bayyana kwace wasu daga naman da ake zargin suna dauke da guba.

“Cikin gaggawa gwamnati ta kwace dukkanin naman da ake zargin suna dauke da guba, tare da tura su dakin gwaje-gwaje domin tabbatar da zargin bayan tattaunawa da yan kasuwar mandate.”

Kara karanta wannan

Kwara: Gwamnati ta fara bincike kan zargin ana sayar da naman shanu mai guba

Sun bayyana cewa nan gaba za su bayyana sakamakon binciken da su ka gudanar da zarar ya kammala, kamar yadda jaridar Punch ta wallafa.

Kwamishinonin sun bukaci al’umma da ka da su ji tsoron komai, su kuma jira sakamakon binciken.

Ana binciken sayar da nama mai guba

Gwamnatin jihar Kwara ta fara bincike kan zargin ana sayar da naman shanu mai dauke da guba a kasuwar Mandate dake Ilorin.

Wannan ya biyo bayan zargin wata cuta ta kashe shanu 33, inda tuni gwamnatin ta ce ta kwace wasu daga naman da ake zargin sun gurbace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel