Annobar Coronavirus: An fara aikin feshin magani a ofishin shugaban kasa
Sakamakon bullar annobar nan mai toshe numfashi, fadar shugaban kasa ta gayyaci kwararru ma’aikatan feshi domin su gudanar da feshi a ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran sassan fadar gwamnatin.
Jaridar Punch ta ruwaito kwararrun sun isa fadar Aso Rock ne da misalin karfe 9:30 na safiyar Alhamis, 26 ga watan Maris kamar yadda wata majiya daga Villa ta tabbatar, wanda ta ce za’a gudanar da feshin a duka lunguna da sako na Villa.
KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Dakarun Sojin Najeriya a shirye suke su garkame Najeriya
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa zuwa karfe 11:15 na safe kuwa, har kwararrun masu feshin sun isa cikin gidan shugaban kasa domin feshi shi gaba daya.
Idan za’a tuna annobar Coronavirus ta shiga fadar shugaban kasa, inda har ta harbi shugaban ma’aikatan fadar, kuma na hannun daman shugaban kasa, Malam Abba Kyari, wanda a yanzu haka yana can a killace a asibitin Gwagwalada.
A wani labarin kuma, kafatanin rundunonin Najeriya na zaune cikin shirin ko-ta-kwana tare da aiki da cikawa domin dabbaka umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na garkame Najeriya da zarar ya bayar da umarnin yin hakan sakamakon yaduwar annobar Coronavirus.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata majiya daga cikin manyan jami’an Sojin kasar nan ta shaida mata cewa an aika ma kowanne rukunin Sojin Najeriya sako daga shelkwatar tsaro ta kasa a kan su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, a ranar Talata.
Haka zalika wasu kafafen sadarwa na yanar gizo sun wallafa wasu takardu da suka yi ikirarin sun fito ne daga shelkwatar tsaro ta kasa dake bayyana shirin Sojoji na mamaye kasar cikin kankanin lokaci domin tabbatar da jama’a kowa ya zauna a gidansa don kauce ma yaduwar annobar.
Wannan rahoto ya fito ne bayan kimanin sa’o’i 72 da ministan watsa labaru, Lai Muhammad ya bayyana cewa kwamitin da shugaban kasa ya kafa don kare yaduwar cutar ta bashi shawarar daukan wasu tsauraran matakai.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng