Kano: SUBEB ta Musanta Zargin Son Zuciya a Jarrabawar Daukar Malaman BESDA
- Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB) ta musanta yin son kai a yanayin rubuta jarrabawar daukar malaman BESDA
- Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf shi ne ya yiwa malaman wucin gadin alkawarin daukar wasunsu aiki a watannin baya
- Akalla kaso 85% ne hukumar SUBEB ta ce sun yi nasara a jarraawar, amma wassu daga kaso 15% ke ganin akwai lauje cikin nadi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano-Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB) ta musanta zargin rashin adalci ko nuƙu-nuƙu a jarrabawar ɗaukar malaman dake ƙarƙashin shirin bayar da ilimi na BESDA.
Tsarin BESDA, wani shirin bayar da ilimi ne ga kowa da kowa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi 17 da babban birnin tarayya Abuja da kuma bankin duniya.
An dauki malaman na wucin gadi a jihohi, inda ake biyansu alawus duk wata.An dauki malaman na wucin gadi a jihohi, inda ake biyansu alawus duk wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma bayan hawan Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin daukar wasu daga malaman BESDA aiki karkashin gwamnatin jihar, wanda hakan ya sa aka rubuta jarrabawa a baya-bayan nan.
Sai dai an jiyo wasu na zargin hukumar SUBEB da bawa wasu shafaffu da mai guraben aikin.
"Ba mu muka duba jarrabawar ba," SUBEB
A zantawar Daraktan yada wayar da kai a hukumar SUBEB, Balarabe Danlami Jazuli ya ce kaso 85% na wadanda suka zauna jarrabawar sun yi nasara.
Daraktan ya kara da cewa a yanzu haka kimanin mutane 5, 632 da su ka yi nasara a jarraawar ake shirin mikawa takardar aiki.
Ya ce su kwantar da hankulansu, an yi jarrabawar bisa adalci, domin ba a hukumar aka duba jarrabawar ba, hukumar dake kula da harkar jarrabawa ta jihar Kano (KERD) ce ta duba ta.
A kalamansa:
"Babu inda ake jarrabawa an yi ace kowa ya ci 100%. Ba a jarrabawa haka."
"Amma ana duba adalcin jarrabawa na adadin waɗanda suka samu nasara, to lallai jarrabawa ta yi kyau kuma ta yi dadi."
Ya ce ba a bana mutum ya yi korafi, amma ya tabbatar da cewa duk wadanda za a dauka, su su ka zauna jarrabawar da gaske.
Gwamnati na shirin sauyawa ma'aikata wurin aiki
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na sauyawa wasu ma'aikatanta aiki zuwa makarantu.
Ma'aikata kimanin 5000 da ke da shaidar karatun malanta ne wadanda za a mayar ajujuwa domin yin aikin da su ka karanta.
Asali: Legit.ng