Da dumin sa: An sace sakataren hukumar ilimi ta SUBEB a jihar Kano

Da dumin sa: An sace sakataren hukumar ilimi ta SUBEB a jihar Kano

- Wasu 'yan bindiga sun sace sakataren hukumar ilimin bai daya (SUBEB) a jihar Kano

- 'Yan bindigar sun sace sakataren a kauyen su na shiye dake karamar hukumar Bunkure a jiya Asabar

- Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kano, Magaji Musa Majiya, a tabbatar da satar sakataren

Wasu 'yan bindiga a jihar Kano sun sace sakataren hukumar ilimin bai daya a jihar, Shiye, a kauyen su shiye dake karamar hukumar Bunkure.

Dan uwa ga sakataren da bai yarda a ambaci sunan sa ba ya tabbatar da cewar wadanda su ka sace yayan nasa sun nemi a biya su miliyan N20 kudin fansa.

"Wadanda su ka sace dan uwana sun kira iyalin sa a waya sun shaida masu cewar da zarar an biya su Naira miliyan N20 za su sake shi," inji dan uwan nasa.

Da dumin sa: An sace sakataren hukumar ilimi ta SUBEB a jihar Kano
An sace sakataren hukumar ilimi ta SUBEB a jihar Kano

Ya cigaba da cewa "ina rokon wadannan 'yan bindiga da su taimaka don Allah su saki dan uwana domin shi ba mai kudi ba ne kuma ba daga dangin masu kudi ya fito ba."

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana cewar an sace sace Shiye ne da misalin karfe 1:00 na rana a kauyen su, Shiye, sannan an sanar da hukumar 'yan sanda da misalin karfe 9:00 na dare.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da amaryar dan majalisar jihar Katsina

Majia ya ce tuni kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabi'u Yusuf, ya aika da jami'an 'yan sanda na SARS zuwa karamar hukumar Bunkure domin ceto sakataren.

"Sun nemi a biya su miliyan N20m amma muna aiki a kan wasu bayanai domin mu ceto shi. Muna fatan nan bada dadewa ba zai dawo ga iyalin sa," Majiya ya bayar da tabbas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel