Gwamnatin Ganduje za ta dauke ma’aikata 5,000, ta maida su aji, su rika koyarwa a makarantu
- Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta sauyawa wasu ma’aikata 5, 000 wuraren aiki
- Wadannan ma’aikata za su rika koyar da dalibai domin a samu isassun malamai
- Ana neman karin malamai yayin da ma’aikata su kayi yawa a MDA da kuma LG
Gwamnatin jihar Kano ta shirya maida wasu ma’aikata 5, 000 masu takardu a harkar malanta zuwa aji domin su rika koyar da ‘yan makarata.
Jaridar Daily Trust ta ce majalisar zartarwa ta jihar Kano ta bada wannan umarni domin karfafa tsarin bada ilmi kyauta da aka shigo da shi a baya.
Kwamishinan harkokin yada labarai, Muhammad Garba, ya ce ta hakan, za ayi maganin matsalar da ake fuskanta na karancin malaman makaranta.
KU KARANTA: Twitter: Ministan harkokin kasar waje ya yi zama da Jakadun ketare
Garba ya fitar da jawabi a ranar Lahadi, 6 ga watan Yuni, 2021, ya ce an dauki wannan matsaya bayan majalisar zartarwa ta yi zama a makon jiya.
Kwamitin musamman da aka kafa domin ya duba tsarin karatun boko a kyauta a jihar Kano ya bada shawarar a canzawa wasu ma’aikata wurin aiki.
Wadanda wannan sauyi zai shafa sun hada masu NCE daga makarantun FCE da ake horas da malamai, da kuma masu Difloma a harkar malanta.
Haka zalika masu takardar shaidar Digiri a bangaren koyarwa watau (B.Ed) za su koma aiki a aji. Jaridun Punch da Premium Times sun tabbatar da haka.
KU KARANTA: Zulum ya sake gina makarantar Chibok da aka sace yara
A cewar kwamishinan akwai ma’aikata 575 da suke da irin wannan takardu da suke aiki a ma’ikatun gwamnati, 3, 712 suna kananan hukumomi.
Daga cikinsu akwai 19 da ke da Digirin PhD, 55 suna da Masters, sannan 1, 100 sun mallaki shaidar B.Ed, 2, 366 sun samu takardar NCE, 10 suna da Difloma.
Masu NCE za su zauna a karkashin SUBEB, wadanda suka mallaki Digiri za su tafi kanana da manyan makarantun sakandare, a cewar Malam Garba.
A jiya mu ke samun rahoto cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta dauki sababbin ma'aikata 10,000 a bangarori daban-daban a lokacin da ake kukan rashin kudi.
Rahoton ya ce wadanda aka dauka aikin sun hada da likitoci, ma'aikatan jinya, malaman jami'a da wasu ma'aikatan masu muhimmanci a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng