Mataimakin Daraktan CBN Ya Zama Sabon Magajin Garin Zazzau
- Mataimakin daraktan CBN, Muazu Nuhu Bamalli, ya zama sabon magajin garin Zazzau da ke jihar Kaduna
- Wannan naɗin da sarkin Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi na zuwa ne bayan rasuwar Alhaji Mansur Nuhu Bamalli
- Bayan haka Sarkin ya naɗa Aliyu Nuhu Bamalli, ƙaninsa a matsayin wanda zai maye gurbin Baraden Zazzau
Zaria, jihar Kaduna - Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya amince da naɗin Mu'azu Nuhu Bamalli, a matsayin sabon Magajin Garin Zazzau.
Muazu Nuhu Bamali, mataimakin darakta a babban bankin Najeriya (CBN) zai maye gurbin marigayi Magajin Gari kuma tsohon jakadan Najeriya a Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli.
Marigayin ya rasu ne ranar Jumu'a 20 ga watan Oktoba, 2023 yana da shekaru 52 a duniya.
Sarkin Zazzau ya naɗa sabon magajin gari
Masarautar Zazzau ce ta tabbatar da naɗin sabon Magajin Gari a wata sanarwa da ta wallafa a Manhajar X, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawunta ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwan ta ce sabon magarin garin da aka naɗa, Muazu Nuhu Bamalli, ba da daɗewa ba Sarkin Zazzau ya naɗa masa rawanin sarautar Baraden Zazzau.
Sanarwan mai taken, "Sabon magajin garin Zazzau ya bayyana," ta ce:
"An naɗa sabon magajin garin Zazzau, shi ne Alhaji Mu'azu Nuhu Bamalli, yayan marigayi magajin gari, Ambasada Mansur Nuhu Bamalli, wanda ya rasu ranar Jumu'a a makon jiya."
Sarki ya naɗa sabon Baraden Zazzau
Bugu da ƙari, Sarkin Zazzau ya kuma amince da nadin Alhaji Aliyu Nuhu Bamalli (Sambo), shugaban ma’aikatan fadar sarki kuma ƙaninsa a matsayin sabon Baraden Zazzau.
Aliyu Bamalli zai maye gurbin mataimakin daraktan CBN bayan ɗaga darajarsa zuwa Magajin Garin Zazzau.
Sanarwar ta kara da cewa, "Dukkan nade-naden za su fara aiki nan take, yayin da za a sanar da ranar da za a yi naɗin rawani daga baya."
Kotu Ta Yanke Hukunci a Ƙarar Aishatu Binani
A wani rahoton kuma Babbar Kotu ta yanke hukunci kan ƙarar da Aishatu Binani ta nemi a dakatar da gurfanar da kwamishinan zaɓen Adamawa.
Dakataccen kwamishinan, Hudu Ari, na fuskantar shari'a a gaban Kotu kan ayyana sakamakon zabe ba bisa ƙa'ida ba.
Asali: Legit.ng