Tsadar Kaya: Yayin da Naira Ke Tashi, Za a Dauki Mataki Kan 'Yan Kasuwa da Kamfanoni

Tsadar Kaya: Yayin da Naira Ke Tashi, Za a Dauki Mataki Kan 'Yan Kasuwa da Kamfanoni

  • Hukumar kare hakkin kwastomomi a Najeriya (FCCPC) ta shirya ladabtar da 'yan kasuwa da ke kara kudin kayayyaki
  • Hukumar ta ce duba da yadda darajar naira ke yin sama, ya kamata kamfanoni da 'yan kasuwa su bar kara kudin kaya
  • Mataimakin shugaban hukumar, Dakta Abdullahi Adamu shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 18 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Yayin da darajar naira ke kara hawa, hukumar kare hakkin kwastomomi (FCCPC) za ta dauki mataki kan tsadar kayayyaki.

Hukumar ya ce ta shirya daukar matakin ne domin tabbatar da cewa kwastomomi ba su sayi kaya da tsada ba a halin yanzu.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Gwamnati ta shirya daukar mummunan mataki kan 'yan kasuwa da ke kara kudin kaya
Hukumar FCCPC ta nuna damuwa kan wasu 'yan kasuwa da kamfanoni da ke kara farashin kaya. Hoto: Sam Makoki.
Asali: Getty Images

Gargadin hukumar kan tsadar kaya a kasuwa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin shugaban riko na Hukumar, Dakta Abdullahi Adamu ya fitar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi ya ce hukumar FCCPC ta umarci jami'anta da su zagaya kasuwanni domin tabbatar da bin ka'idar farashin kaya.

Ya ce za su dauki mataki kan dukkan 'yan kasuwa da kamfanoni da ke kara farashin kayayyaki ba bisa ka'ida ba.

Tsadar kaya: Wane mataki FCCPC ta dauka?

"Hukumar ta himmatu wurin wayar da kan jama'a domin sanin hakkinsu da kuma zaben kayan da suke bukata."
"Za mu samar da wata kafa ta wayar da kan jama'a musamman dangane da karin farashin kaya babu ka'ida tare da dabarun zakulo su da kuma kai rahotonsu."

- Adamu Abdullahi

Sanarwar ta ce za ta ci gaba da saka ido kan kamfanoni da 'yan kasuwa da ke kara farashin domin daukar matakin shari'a.

Kara karanta wannan

Badakalar N84bn: Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC na cafke Yahaya Bello

Dangote ya rage farashin litar dizal

A wani labarin, kun ji cewa Attajiri Aliko Dangote ya rage farashin litar man dizal daga N1,200 zuwa N1,000 a Najeriya.

Dangote ya dauki wannan matakin ne kasa da watanni uku bayan rage farashin daga N1,650 zuwa N1,200 kan kowace lita.

A baya, attajirin ya ce rage farashin man dizal shi ne kadai hanyar dakile hauhawan farashin kaya da ake fama da shi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel