Daga cikin Mu’ijizozin manzon Allah ﷺ.

Daga cikin Mu’ijizozin manzon Allah ﷺ.

Manzon Allah ﷺ , fiyyayen annabawa kuma cikamakin manzanni ya aikata wasu mu’ijizozi da ya kamata kowani musulmi ya sansu.

Game da cewar wata shafin yanar gizo mai suna, Musliminc, akwai mui’jizozi 11 wanda ya aikata

1. Badda gani

Lokacin da manzon tsira ﷺ ya nufi yin hijra zuwa kasar Madina, kabilun garin Makka sun hada baki domin kashe shi. Sun yi ma gidansa zobe amma a haka ya fita gabansu bau ganshi ba.

2. Rakumin da makale cikin yashi

Yayinda manzon Allah ﷺ ya fara tafiya tare da sahhabinsa Abubakar, akwai wani mai suna Suraka bin Malik wanda ke biye da su.

Kawai yayinda Suraqa ya kusa cimmusu, sai rakuminshi ya turke cikin yashi. Surqa ya cire rakumin amma ta sake turkewa, lokacin ya fahimci cewa cut aba zai samu manzon Allah ba.

KU KARANTA: Adadin musulman duniya zai tserewa na Kiristoci

3. Magana da Aljanu

A wata hadisi, wani aljani mai suna ‘Hama’ ya zo cikin siffan wani dattijo rike da sanda; sai ya karbi addinin musulunci. Manzon Allah ya karanta masa wasu ayoyin Alkur’ani wanda ya karanta kafin ya wuce.

4. Koramai sun gudana daga cikin hannunsa

Lokacin da manzon Allah tare da sahabbai kimanin 300 suka kai wani wuri mai suna Zawra. Sai lokacin sallah yayi amma babu ruwan alwala. Sai manzon Allah ya umrucesu da su samu ruwa kadan, sai ya sanya hannunsa kawai sai korami ya fara gudana daga hannunsa.

5. Tafiyar Is’ra’I da mi’iraji

Tafiyar da manzon Allah yayi zuwa birnin kudus kuma yaje ya gana da Allah cikin dare daya.

6. Rabewar wata gida 2

Yayinda mushrikai suka nace manzon Allah ya nuna musu mui’jiza. Sukace idan zai iya, ya raba musu wata gida 2.

7. Maganar itace, dutsuna, dabbobi da manzon Allah

8. Warkar da marasa lafiya

A wata hadisi, an harbi wani sahabi cikin idanuwansa. Sai manzon Allah ya sanya hannu ya warkar masa da shi

9. Mafi girman mui’jizozin manzon Allah shine Alkur’ani

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel