Gwamna Zulum ya kai ziyara garin Baga, ya ba talakawa sama da 4000 tallafin kudi
- Gwamnan jihar Borno ya tallafawa mazauna a garin Baga da ababen more rayuwa
- Legit Hausa ta tattaro cewa, gwamnan ya kwana a garin na Baga domin aikin agaji
- Ya raba wa mazauna sama da 4,000 da kayayyaki duk da ruwan sama da aka yi a ranar
Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara garin Baga, inda ya zarce zuwa babban asibitin Ibrahim Dada, kuma yayi tattauna da dukkan ma'aikatan kiwon lafiya a asibitin.
Gwamnan ya zaga cikin asibitin domin gane wa idonsa yadda al'amura ke tafiya a cikinsa, da kuma duba yadda kayayyakin cikinsa suke, yayin da daga baya ya tattauna da ma'ikata 27 a asibitin.
Zulum ya kuma shaida musu cewa gwamnatinsa a shirye take ta tallafa wa 'yan asalin karamar hukumar Kukawa 50, wadanda ke son ci gaba da karatunsu, musamman matasa masu son zuwa kwasa-kwasai a fannin likitanci da sauran darussan da suka danganci hakan.
Cikin wata sanarwa da gwamna Zulum ya fitar ta shafinsa na Facebook, Legit Hausa ta gano cewa, gwamnan00 ya gano cewa asibitin ba shi da manyan lititoci, Zulum ya ba da umarnin daukar duk wani likitan da ke son zama da aiki a garin, wanda a lokacin aka samu.
Hakazalika ya ba ma'aikatan kiwon lafiyar kudade wasu N20,000 wasu kuwa N50,000 da buhunnan shinkafa. Masu aikin sa kai a asibitin suma an basu N10,000.
Zulum ya kwana a garin Bama, ya tallafawa talakawa sama da 4,000
Gwamnan na jihar Borno ya kuma kwana a garin Baga a karamar hukumar Kukawa, inda ya zauna domin gudanar da ayyukan jin kai ga mazauna garin, ya kuma tallafawa mazauna 4,798 a garin da ababen more rayuwa.
Sanarwar ta ce:
"Duk da ruwan sama mai yawa a Baga, Zulum bai tsaya ba. A maimakon haka ya dauki lokacinsa don ci gaba da tafiyarsa ta jin kai ta hanyar rarraba abinci, sutura da tsabar kudi ga mutane.
"Daga cikin adadin masu cin gajiyar garuruwan biyu, mata 2,905, kowannensu ya sami buhun shinkafa, buhun masara, murfin kunsa da tsabar Naira 10,000, yayin da maza 1,893 suka karɓi buhun shinkafa, buhun masara, da tsabar kudi Naira 10,000."
An samar wa sojojin da ke yakar 'yan Boko Haram jirgin yawo lokacin hutu
A wani labarin, Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a samar da jirgin saman zirga-zirga ga sojoji da manyan jami'ai a fagen daga wadanda aka ba izinin ficewa na wucin gadi da nufin zuwa ganin danginsu yayin da suke kan aiki.
Jaridar TheCable ta ba da rahoton cewa izinin ficewar, a yaren sojoji, izini ne na barin sashin aiki na dan wani lokaci.
Legit.ng ta tattaro cewa mafi yawan sojoji da jami'ai da aka tura daga sassa daban-daban na kasar zuwa rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabas suna tafiya daruruwan kilomita lokacin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi domin ganin danginsu.
Asali: Legit.ng