Hukumar NDLEA Ta Kai Samame Legas da Ogun, Ta Lalata Haramtattun Kwayoyi da Dama

Hukumar NDLEA Ta Kai Samame Legas da Ogun, Ta Lalata Haramtattun Kwayoyi da Dama

  • Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kai samame a wasu yankunan jihohin Legas da Ogun
  • Yayin samamen, hukumar ta yi nasarar kamawa tare da lalata kilo 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi a ranar Talata da ta wuce
  • Shugaban hukumar ta kasa, Buba Marwa ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su cigaba da goyon bayan ayyukansu domin kawar da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar lalata haramtattun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da shahararren dan kasuwa Cubana bisa zargin cin zarafin Naira

NDLEA
Hukumar NDLEA ta lalata kwayoyin da ta kama ne a bainar jama'a domin hakan ya zama izina ga wasu. Hoto: Stefan Heunis
Asali: Getty Images

Hukumar ta samu nasarar ne ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

Adadin kwayoyin da NDLEA ta lalata

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi da ta kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta lalata haramtattun kwayoyin ne da ta kama a bainar jama’a a Badagry da ke jihar Legas.

Jawabin shugaban Hukumar NDLEA

Shugaban hukumar ta kasa, Mohamed Buba Marwa ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin kotu ne.

Buba Marwa ya yi kira domin samun karin goyon bayan jama'a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ganduje: Hukumar PCACC ta kaddamar da sabbin tuhume tuhume a kan tsohon gwamnan Kano

Marwa ya kara da cewa kwayoyin da suka kama nau'o'i ne daban-daban da suka hada da koken, kanabis da tramol.

Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, malamai, kungiyoyi da sauran wadanda suka shaida lalata kwayoyin.

Kiran NDLEA ga al'ummar Najeriya

Yayin da yake tabbatar da cewa NDLEA ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawo karshen matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a kasar, shugaban ya yi kira ga al'umma da su kara tallafawa ayyukan hukumar.

Gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu wanda ya samu wakilcin shugaban karamar hukumar Badagry West, Mista Olusegun Onilude ya bayyana jin dadinsa da kokarin hukumar na shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi a kasar nan.

Ya kuma godewa hukumar kan yadda ta dauki wayar da jama'a a kan yaki da muggan kwayoyi zuwa makarantu da wurare mabanbanta a fadin jihar Legas.

Kara karanta wannan

Mahajjata 135 sun rasa damar zuwa aikin hajji a jihar Filato bayan karin kudin kujera

NDLEA ta kai samame jihar Kano

A wani rahoton kuma, kun ji cewa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu gagarumin nasara wajen yaki da ta'ammalli da miyagun kwayoyi a jihar Kano.

A cikin watanni 3, ta kama mutane 319 da ake zargi suna da hannu dumu-dumu cikin harkar kwaya a Kano, 14daga cikinsu mata ne sauran 305 din kuma maza ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel