Mahajjata 135 Sun Rasa Damar Zuwa Aikin Hajji Daga Filato Bayan Karin Kudin Kujera

Mahajjata 135 Sun Rasa Damar Zuwa Aikin Hajji Daga Filato Bayan Karin Kudin Kujera

  • Maniyyata aikin hajjin bana guda 135 ne suka rasa damar zuwa sauke farali daga jihar Filato sakamakon karin kudin aikin hajjin bana
  • Jami’in yada labarai na hukumar jin dadin alhazai a jihar Filato, Yasir Isma’il, ne ya bayyana adadin yayin hira da 'yan jarida
  • Ya kuma bayyana dalilai da suka sa maniyyatan basu samu damar shiga cikin masu zuwa aikin hajjin banan ba duk da cewa sun kawo cikon kudin nasu zuwa hukumar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Filato ta ce maniyyata 135 da suka fara biyan kudin aikin hajji ba za su samu shiga aikin hajjin bana ba.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: EFCC ta bankado wasu makudan kudaden tallafin Korona da aka sace a mulkin Buhari

Hakan na zuwa ne biyo bayan karin kudin da hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) tayi a watan Maris.

Ka'aba Hajj
Maniyyata za su rasa zuwa hajjin bana daga Filato Hoto: Ahmad Alrubaye
Asali: Getty Images

Hukumar ta kara kudin jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya na shekarar 2024 da Naira miliyan 1.9, daga Naira miliyan 4.9 zuwa Naira miliyan 6.8.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta kuma sanya ranar 28 ga watan Maris a matsayin wa’adin da aka ba wa maniyyatan kammala biyan karin da aka musu.

Hajji: Abin da ya faru a Filato

Mutanen da abin ya shafa daga jihar Filato a ranar Juma’ar da ta gabata sun garzaya zuwa hukumar alhazai ta jihar domin kammala biyan kudaden.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa ba su samu jami’an da za su karbi kuɗin ba a farfajiyar hukumar, cewar jaridar Daily Nigerian.

Martanin hukumar aikin hajji

Jami’in yada labarai na hukumar, Yasir Isma’il, a wata tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Trust, ya ce wadanda abin ya shafa sun gaza biyan kudaden har lokacin da wa’adin biyan kudin ya kare.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Jami'in dan sandan da ya yi barazanar sheke farar hula da bindiga ya shiga hannu

Ya ce tuni NAHCON ta kammala buga jerin sunayen wadanda za su halarci aikin Hajjin bana, wanda hakan ya sa hukumar ta kasa samun karin kujeru daga jihar.

Isma’il ya bayyana cewa, duk da cewa mahajjata da dama ba su iya cika wa’adin farko na ajiye kudin aikin hajjin ba, amma gwamnatin jihar ta amince da ba da lamuni na Naira biliyan biyu domin samun cike gurbin maniyyata da aka bawa jihar.

NAHCON ta kara kudin aikin hajji

A wani rahoton kuma, kun ji cewa, hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya da Naira 1,918,032.91.

Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa hakan ya faru ne saboda tashin dala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel