"A Taimaka Mana": Wasu Maniyyatan Arewa Sun Roƙi NAHCON Alfarmar Zuwa Hajji
- Wasu daga cikin mahajjatan jihar Filato su roƙi NAHCON ta taimaka ta karɓi cikon N1.9m na aikin hajji duk da wa'adi ya ƙare
- Mahajjatan sun bayyana irin faɗu tashin da suka yi kafin su samu damar haɗa kudin amma sun kai an faɗa masu ba za a karɓa ba
- Tun farko dai NAHCON ta ƙara N1.9m kan kowace kujerar hajji kuma ta ba da wa'adin kwanaki huɗu ga kowane alhaji ya cika
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Filato - Maniyyata daga jihar Filato a aikin hajjin bana 2024 sun roƙi hukumar jin daɗin alhazai ta kasa (NAHCON) ta karɓi cikon kuɗin kujera N1.9m.
Mahajjatan jihar da ke Arewa ta Tsakiya sun buƙaci NAHCON ta taimaka ta karɓi wannan cikon duk da wa'adin da ta gindaya na kammala biyan kudin ya wuce.
Wa'adin biyan kudin aikin Hajji
Idan ba ku manta ba NAHCON ta ƙara kuɗin kujerar zuwa sauke farali a 2024 daga N4.9m zuwa N6.8m a watan Maris da ya shige.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, wannan ƙarin kuɗi da NAHCON ta yi ya jefa da yawa daga cikin maniyyata cikim halin rashin tabbas da fafutukar cika kuɗin.
Duk da wa’adin kwanaki hudu da NAHCON ta bayar na kammala biyan kudin, maniyyatan da dama ba su samu damar yin cikon ba saboda ƙarancin lokaci.
Hajji: Maniyyata sun roƙi NAHCON
Isa Abubakar, daya daga cikin masu shirin zama mahajjatan jihar Filato ya bayyana takaicinsa, yana mai cewa:
"Cikon ya faɗo mana a yanayi mai wuya, lokacin da NAHCON ta bayar na cika kuɗin ya yi kaɗan, muna ts faman haɗa kuɗin, har da sayar da wasu kadarorin mu."
"Amma duk da wannan ƙoƙarin da muka yi, sun ƙi karɓan cikon kuɗin hajji da muka kai masu, wannan ba ƙaramin abin takaici bane."
Abubakar Sa’idu ya yi magana mai kama da wannan, inda ya bayyana kalubalen tattalin arzikin da masu niyyar zuwa aikin Hajji bana ke fuskanta.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta sa baki ka da a hana waɗannan bayin Allah damar zuwa sauke farali a wannan shekarar.
Muktar Magaji, daraktan ayyuka na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Filato ya bayyana cewa tuni NAHCON ta kammala haɗa sunayen wadanda za su halarci aikin hajjin 2024.
NAHCON ta faɗi yawan alhazan bana
A wani rahoton kuma Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta yi ƙarin haske kan shirye-shiryenta dangane da aikin Hajjin bana na shekarar 2024
Hukumar ta bayyana cewa a wannan shekarar maniyyata mutum 50,000 za su sauke farali a ƙasa mai tsarki.
Asali: Legit.ng