Gwamnonin Arewa 10 Za Su Halarci Taron Tsaro a Amurka
- Cibiyar Afirka da ke karkashin Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta gayyaci gwamnoni 10 daga arewacin Najeriya zuwa taron tsaro
- Taron wanda za a gudanar da shi ne a birnin Washington DC daga ranar 23 zuwa 25 ga Afrilu, 2024 zai karkata kan matsalolin tsaro a Arewa
- Kamar yadda ata sanarwa ta nuna, gwamnonin da aka gayyata za su wakilci shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - An gayyaci gwamnoni 10 daga arewacin Najeriya, masu wakiltar shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya zuwa wani taro na zaman lafiya da tsaro a Amurka.
Manufar taron tsaron cibiyar USIP
Taron wanda aka gayyaci gwamnonin, za a gudanar da shi ne a birnin Washington DC daga ranar 23 zuwa 25 ga Afrilu, 2024, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Ibrahim Kaula Mohammed, mai taimaka wa Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina kan harkokin yada labarai, da ya fitar a ranar Talata.
Mohammed ya bayyana cewa Cibiyar Afirka da ke karkashin Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka (USIP) ta shirya taron da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya.
Jerin gwamnoni 10 da aka gayyata
The Cable ta jero gwamnonin da aka gayyata da sunka hada da Dikko Umar Radda (Katsina), Uba Sani (Kaduna), Abba Kabir Yusuf (Kano), Nasir Idris (Kebbi) da Umar Namadi (Jigawa).
Sauran sun hada da Ahmad Aliyu (Sokoto), Dauda Lawal (Zamfara), Hyacinth Alia (Benue), Mohammed Bago (Neja) da Caleb Mutfwang (Filato).
Sanarwar ta bayyana cewa taron na da nufin bunkasa karfin gwamnoni wajen yaki da tashe-tashen hankula da samar da zaman lafiya a fadin Najeriya ta hanyar tattaunawa da kuma hadin gwiwa.
"Wannan gayyata dai na da nasaba da muhimmiyar rawar da gwamnonin ke takawa wajen dakile barazanar tsaro da samar da zaman lafiya a jihohinsu."
- A cewar sanarwar.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Zamfara
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun samu nasara a wani hari da suka kai kan 'yan bindiga a jihar Zamfara.
A cewar rundunar, sojoji sun kashe akalla 'yan bindiga 15 tare da kwato makamai da babura 10, wanda ke kara nuna hazaka da sadaukarwar dakarun.
Asali: Legit.ng