Dole mu gyara ma'aikatar karafa ta Ajaokuta ko da zamu ciyo bashi ne - Yakubu Dogara

Dole mu gyara ma'aikatar karafa ta Ajaokuta ko da zamu ciyo bashi ne - Yakubu Dogara

- An kashe biliyoyin daloli a kan Ajaokuta, amma har yanzu babu wani abu da take yi

- Ajaokuta na jihar Kogi ne, kuma manyan karafa ake sa rai zata sarrafa

- Yakubu Dogara na fatan gwamnati zata tayar da komadar ta

Dole mu gyara ma'aikatar karafa ta Ajaokuta ko da zamu ciyo bashi ne - Yakubu Dogara
Dole mu gyara ma'aikatar karafa ta Ajaokuta ko da zamu ciyo bashi ne - Yakubu Dogara

Malam Yakubu Dogara, na hdu a kasar nan, wanda ya fito daga jihar Bauchi, ya bayyana cewa gwamnatinsu ta APC zata tashi komadar kamfanin tama da karafa na Ajaokuta, wanda ke fuskantar matsaloli tun da aka kafa shi a shekaru kusan 40 da suka wuce.

Kamfanin na Ajaokuta dai, ya ishi kasar nan takaici, bayan da gwamnatoci a baya suka singi narka kudade cikinsa amma abin ya faskara. Ya qi ya motsa kuma yaki sayuwa.

A yanzu dai Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilai, a hirarsa da Jaridar Premium Times, ya ce dole ne gwamnati ta tashi wannan kamfani mai muhimmanci koda kuwa bashi zata ci.

DUBA WANNAN: Wani saurayi ya kai matarsa kotu, bayan wai cewa tayi masa cikin shege

A jihar Kogi aka kafa kamfanin, kuma an sha sayar da shi amma ana kwacewa domin rashin ganin wani ci gaba kan samar da karafan da aka sa rai zaiyi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel