Masu shigo da kaya daga kasashen waje ke nakasa Nigeria - Ogbeh

Masu shigo da kaya daga kasashen waje ke nakasa Nigeria - Ogbeh

- Ministan noma ya ce masu shigo da kaya daga kasashen ketare su ne manyan makiyan Nigeria a kokarin da kasar ke yi na bunkasa amfani da kayayyakin cikin gida

- Ya ce kayayyakin da ake shigowa da su kasar kamar irinsu tsinke sakutar hakori, sukari, kayan lambu da fensiri na matukar ciwa gwamnati tuwo a kwarya

- A baya bayan nan jakadan kamfanin giya na Champagne a Nigeria ya ce 'yan Nigeria na sahun gaba wajen shan giyar Champagne a fadin duniya

Ministan noma, Mr Audu Ogbeh, ya ce masu shigo da kaya daga kasashen ketare su ne manyan makiyan Nigeria a kokarin da kasar ke yi na bunkasa amfani da kayayyakin cikin gida. Ministan noma da bunkasa karkara, Chief Audu Ogbeh ya bayyana hakan a Abuja a lokacin da ya gabata gaban kwamitin majalisar zartaswa kan noma nomin kare kasafin da aka warewa ma'aikatar.

Ya ce kayayyakin da ake shigowa da su kasar kamar irinsu tsinke sakutar hakori, sukari, kayan lambu da fensiri na matukar ciwa gwamnati tuwo a kwarya, a kokarin da ta ke yi na tabbatar da cewa 'yan Nigeria sun sayi kayayyakin da aka sarrafa su a cikin kasar.

"Abun dubawar a nan shine, kwandon tumaturi yanzu na kasa da N2,000.Manoma na rasa kudi saboda masu sarrafa su basu da isassun kudaden da za su bude ma'aikatu. A yanzu dai an fara aiki da wasu kamfanoni guda biyu, muna sa ran nan da karshen wannan shekarar za mu dakatar da masu shigo da tumaturin da aka sarrafa.

KARANTA WANNAN: Dan takarar gwamnan Yobe a PDP ya ce ba zai kalubalanci nasarar APC a kotu ba

Masu shigo da kaya daga kasashen waje ke nakasa Nigeria - Ogbeh
Masu shigo da kaya daga kasashen waje ke nakasa Nigeria - Ogbeh
Asali: Depositphotos

"Babbar matsalar kawai shine, da zaran kayi haka sai ka ga ka samu makiya; hatta shigo da shinkafa kasar da muke kokarin ragewa ya haddasa mana karuwar makiya, manyan makiya, irin mutanen da ke iya kisa idan sun samu dama saboda suna ganin kana lalata masu kasuwanci.

"Bai kamata mu dauki wannan da wasa ba. Wadannan mutanen sun kwace tattalin arzikin kasar. Wannan karnin bai samu karbuwa ba saboda yana kokarin dakatar da shigo da kaya kasar tare da karkatar da arzikin kasar zuwa ga wani bangare.

"Ni na san abun da nake fada saboda na kasance a cikin wannan kasuwancin tsawon shekaru 41. Muna shigo da sukari, kyallen goge zufa, tsinken sakucen hakori, har ma da fensiri.

"A baya bayan nan na karanta a wata jarida cewar jakadan kamfanin giya na Champagne a Nigeria ya ce 'yan Nigeria na son more rayuwa. Mu ne a sahun gaba wajen shan giyar Champagne a fadin duniya," a cewar ministan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel