Daga gwada mijina da aminiyata, yanzu gashi nan yana shirin auro mini ita - Mata ta koka

Daga gwada mijina da aminiyata, yanzu gashi nan yana shirin auro mini ita - Mata ta koka

- Wata mata mai suna Betsy ta bayyana yadda kawarta da mijinta suka ci amanarta har zasu angwance

- A saboda rashin haihuwa ne sirikarta ta fara bukatar mijinta ya kara aure, duk da kuwa ita ke ciyar da gidan

- Bayan hada kawarta da mijinta don gano ko yana neman mata, kawai sai katin biki ta gani don kuwa sun gama sasanta kansu

Wata mata mai suna Betsy ta bayyana labarin cin amanarta da aka yi. Betsy tace sunyi aure da mai gidanta mai suna Ken kusan shekaru hudu da suka gabata, amma basu samu haihuwa ba. A cikin shekarun kuwa ita ke ciyar da kanta tare da mijin nata.

A cikin kwanakin nan ne mahaifiyar mijinta ta fara matsa masa a kan ya kara aure saboda ta kasa haifar mata jikoki. “A lokacin da na gano hakan, raina ya matukar baci. Duk da cewa ni ke ciyar da gidan, amma mahaifiyar mijina bata ganin hakan. Ba zai yuwu ina aiki tare da ciyar da gidan ba amma basa bayana.”

“Bayan kamar watannin shida ne Ken ya fara canza hali, kuma na yanke hukuncin hada shi da wata kawa ta da muka yi sakandire da ita. Ta haka ne na yanke shawarar hada shi da Alice don gano cewa ko yana mu’amala da wasu matan na waje.”

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Miji ya yiwa surukarsa gunduwa-gunduwa

Betsy ta bayyana cewa wannan ne lamarin da tafi dana sani a duk fadin rayuwarta. Ba tare da saninta ba, mijinta Ken ya samu karin girma wajen aiki kuma kudinshi ya kara yalwata. Amma saboda bacin rai Betsy ta kasa fahimtar hakan.

“A yayin da na cusa Alice wajen mijina, ashe faduwa ce ta zo dai-dai da zama. Daga nan ne ya dinga wa Alice ruwan kudi, ita kuwa ta bayyana mishi yadda muka yi da ita.

“A halin yanzu dai Alice zata aura mijina. Ya ce na cika tinkaho kuma bana mutunta shi. Ya ce Alice zata iya yi mishi abinda yake so. Ina neman shawara, ya zanyi don dawo da Ken gareni?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel