Rana-bata-karya: Gobe jam'iyyar adawa ta PDP zata zabe sabbin shuganni
Akalla wakillan zabe kusan 3,000 ne zasu jefa kuri'ar su gobe a yayin babban gangamin jam'iyyar adawa ta PDP wajen zabar sabbin shugabannin ta da za'a gudanar a filin taro na Eagle Square dake a garin Abuja.
Yanzu haka dai kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu sun tabbatar mana da cewa tuni dai filin da za'a gudanar da ganganmin ya dauki harama inda aka kawatashi da ababen sha'awa da dama.
KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta fara zawarcin wasu gwamnoni
Legit.ng dai ta samu cewa wannan taron dai na zaman irin sa na farko da jam'iyyar zata gudanar tun bayan faduwar da ta yi a zaben da ya gabata na 2015 inda jam'iyyar APC ta ka da ta.
Haka ma dai mun samu cewa Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar adawa ta PDP watau Chairman of the Board of Trustees (BoT) a turance Sanata Walid jibrin ya bayyana cewa jam'iyyar ta adawa na nan na dakun sauraron dawowar tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran mukarraban sa.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng