Rai Baƙon Duniya: Jami'ar Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Babban Rashi a Birnin Abuja

Rai Baƙon Duniya: Jami'ar Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Babban Rashi a Birnin Abuja

  • Jami'ar rundunar sojin Najeriya ta shiga jimami da alhini sakamakon rasuwar ɗaya daga cikin manyan lakcarorinta
  • Birgediya Janar Ali Williams Butu mai ritaya ya rasu yana da shekara 58 a duniya a wani asibitin kuɗi a Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya
  • Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya mayar da martani kan mutuwar, inda ya bayyana ta da babban rashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Birgediya Janar Ali Williams Butu mai ritaya, wanda ya kusa zama Farfesa a fannin ilmin wurare kuma shugaban tsangayar kimiyyar muhalli a jami'ar sojoji ya rasu.

Marigayin, wanda ke aiki a jami'ar rundunar sojoji da ke Biu a jihar Borno ya rasu ne ranar Jumu'a, 12 ga watan Fabrairu, 2024.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Marigayi Janar Butu.
Malami a jami'ar sojoji da ke jihqr Borno ya rasu Hoto: Brig. Gen Ali Williams Butu
Asali: Twitter

Janar Batu ya fito ne daga yankin ƙaramar hukumar Takum a jihar Taraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa za a yi jana'izar marigayin ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, 2024 a ƙauyen Butu da ke kan titin Takum-Kashimbilla a ƙaramar hukumar Takum a Taraba.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, Janar din soja mai ritaya ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya yana da shekaru 58 a duniya.

Gwamnan Taraba ya tabbatar da mutuwar

Da yake ta'aziyya, Gwamna Agbu Kefas na Taraba ya bayyana mutuwar Butu a matsayin rashi mara daɗi da raɗaɗi, inda ya ce an yi babban rashi ga jihar da ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya faɗi haka ne a wata sanarwa da mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin sadarwa ta zamani, Emmenuel Bello, ya fitar.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

Gwamna ya ce Butu ya rasu ne a daidai lokacin da jihar da sauran al’ummar Najeriya ke matukar bukatar hikima da shugabancinsa.

"Duk da nasarorin da Janar Butu ya samu, ya kasance mutum ne da ya yi rayuwa abin kwatance kuma ya kasance mai tawali’u a tsawon rayuwarsa a duniya," in ji shi.

Nasarorin sojoji a makon jiya

A wani rahoton na daban Dakarun sojojin Najeriya sun halaka ƴan bindiga 188 tare da kama wasu 330 a cikin makon da ya gabata a Arewacin ƙasar nan.

Kakakin hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya ce ga dukkan alamu sojoji sun kamo hanyar kawo ƙarshen duk wani nau'in ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel