An Shiga Jimami Bayan Jaruman Fina-finai 4 Sun Rasa Rayukansu Yayin Hatsarin Jirgin Ruwa

An Shiga Jimami Bayan Jaruman Fina-finai 4 Sun Rasa Rayukansu Yayin Hatsarin Jirgin Ruwa

  • Masana'antar fina-finan Nollywood ta shiga jimami bayan sanar da mutuwar jarumanta guda hudu sanadin hatsarin jirgin ruwa
  • An tabbatar da cewa jaruman sun mutu ne yayin da suke cikin jirgin ruwan bayan dawowa daga daukar shirin fim
  • Lamarin ya faru ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu kamar yadda mai shirya fina-finai, Samuel Olatunji ya tabbatar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Jaruman Nollywood akalla hudu ne suka rasa rayukansu a yau Laraba 10 ga watan Afrilu.

Jaruman hudu sun mutu ne yayin hatsarin jirgin ruwa Baya ya kife da su a cikin kogi kamar yadda mai shirya fina-finai, Samuel Olatunji ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Daso, an sanar da mutuwar wata matashiyar jarumar fina-finai

An shiga jimami bayan mutuwar jaruman fina-finai 3 a hatsarin jirgin ruwa
An sanar da mutuwar jaruman fina-finan Nollywood 3 sanadin hatsarin jirgin ruwa. Hoto: @jnrpope.
Asali: Instagram

Mene musabbabin mutuwar jaruman?

Daga cikin jaruman da suka mutu yayin hatsarin jirgin ruwan akwai Pope Odonwodo wanda aka fi sani da 'Junior Pope', cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Jarumai guda hudu sun mutu ciki har da Junior Pope a bayan dawowa daga fim."
"Jaruman hudu sun mutu ne bayan kwale-kwale ya kife a kogin Anam kuma tuni aka zakulo gawarwakinsu duka."
"Wannan babban abin takaici ne a masana'antar Nollywood, muna cikin alhini tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu."

- Samuel Olatunji

Har zuwa karkare wannan rahoton, ba a samu sunayen sauran jaruman da suka mutu ba.

An karyata mutuwar Junior Pope

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa jarumi Junior Pope ya farfado bayan kai shi asibiti da aka yi tare da ba shi kulawa.

The Nation ta ruwaito shugaban kungiyar jaruman, Ememka Rollas inda ya ke cewa Pope ya na raye kuma ya na karbar kulawa a asibiti.

Kara karanta wannan

Ruwan sama ya lalata gine-gine tare da raba mutane 3,000 da gidajensu a Kogi

Jarumar Nollywood ta riga mu gidan gaskiya

A baya, mun kawo muku labarin cewa An shiga jimami bayan sanar da rasuwar jarumar fina-finan Nollywood, Adejumoke Aderounmu da shekaru 40.

Aderounmu ta yi kaurin suna a shirin fim mai dogon zango na ‘Jenifa’s Diary’ wanda ta fito a shirin a matsayin Esther.

Dan uwan marigayiyar, Adeola Aderounmu shi ya tabbatar da mutuwar tata a jiya Litinin 8 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel