'Yan Shi'a Za Su Dauki Fansar Rayukan 'Yan Uwansu da Aka Hallaka? El-Zakzaky Ya Magantu
- Kungiyar Shi'a a Najeriya ta ƙaryata jira cewa ta na shirin daukar mataki kan kisan 'yan uwansu da aka yi a Kaduna
- Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky shi ya tabbatar da haka inda ya ce babu kamshin gaskiya a labarin
- Wannan na zuwa ne bayan kisan matasa bakwai 'yan kungiyar da aka yi a jihar Kaduna kwanaki takwas da suka wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar IMN a Najeriya da aka fi sani da Shi'a ta ƙaryata cewa za ta dauki mataki kan kisan 'yan ƙungiyar.
Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce babu wani shiri na dakar fansa kan abin da ya faru.
El-Zakzaky ya karyata jita-jitar daukar fansa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa Isah Hassan Mshelgaro ya fitar a madadin kungiyar ta kasa, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mshelgaro ya ce rundunar 'yan sanda ta yada wani sako da ke nuna cewa 'yan Shi'a na shirin daukar mataki bayan kisan 'yan uwansu da aka yi a Kaduna.
Kungiyar ta ce ana yada sakon ga sauran ofisoshin rundunar 'yan sanda domin a yada shi ya zagaya ko ina.
El-Zakzaky ya kadu da labarin daukar fansar
Ta ce Sheikh Zakzaky ya kadu da samun sakon da 'yan sandan ke yadawa kan shirin daukar matakin.
"Muna son sanar da al'umma cewa babu wani shiri na daukar fansa kan kisan 'yan uwanmu guda bakwai da aka yi a jihar Kaduna kan 'yan sanda ko wata kungiyar ko jama'a."
"Wannan abin kunya ya fito ne daga hedkwatar 'yan sanda daga jihar Borno wacce nisanta da jihar Kaduna ya kai kilomita 800."
- Cewar kungiyar
Kungiyar ta kara da cewa a shekarun bayan an hallaka mambobinta da dama amma ba ta dauki mataki ba, sai dai kuma hakan bai kuma ba ya na nufin ba su san me suke ba.
Ta ce duk abubuwan da suka faru akwai ranar da adalci zai bayyana amma dai ba za su taba mantawa ko yafewa ba, cewar Peoples Daily.
Legit Hausa ta tattauna da wani ɗan kungiyar kan wannan sanarwa da kungiyar ta fitar a jiya Asabar
Ali Umar Muhammad a Gombe ya ce za su bi umarni bisa sanarwar da aka fitar saboda lafiya.
"Amma dai kamar yadda aka fada ba za mu taba manta abin aka yi mana a baya ba."
- Ali Umar
Ya bukaci saka wadanda suka rasa ransu cikin addu'o'i domin samun rahama a gare su.
An kara da 'yan sanda da Shi'a
Kun ji cewa cewa rigima ta barke a jihar Kaduna yayin da aka kaure tsakanin 'yan Shi'a da rundunar 'yan sanda.
Rahotanni sun tabbatar da cewa akalla 'yan kungiyar bakwai aka hallaka yayin rikicin a Zaria da cikin Kaduna.
Asali: Legit.ng