Yan Daba 200 Sun Tuba, Sun Zama Nagari, inji Gwamnan Kano
- Gwamnatin Kano ta ce ta ƙuɗiri aniyar magance ayyukan daba da bangar siyasa tsakanin matasan jihar domin samar da ci gaba
- Wannan batu na zuwa ne yayin da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi hawa zuwa fadar gwamnatin a yau Juma'a
- Mai martaba Sarkin ya ce su ma iyaye sai sun dinga sa ido kan mu'amalar yaransu domin bayar da tasu gudunmawar wajen magance daba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta ce kimanin tubabbun ƴan daban 200 a jihar ne yanzu haka suka zama ƴan ƙasa na gari.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan ga mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero yayin da ya yi yawa zuwa fadar gwamnatin a yau Juma'a kamar yadda Nigerian Tribune ta wallafa.
Ya ce daga waɗanda rundunar ƴan sandan Kano ta kama kimanin 200, akwai ɓarayin waya da ƴan bangar siyasa, kuma dukkanninsu yanzu suna bayar da gudummawa wajen ci gaban Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muna yaƙi da daba, inji Gwamnan Kano
A cewar Abba Kabir Yusuf tun bayan bayan tabbatar masa da kujerar gwamnan Kano gwamnatinsa ta duƙufa wajen kakkaɓe ayyukan daba da bangar siyasa tsakanin matasan jihar.
Gwamnan ya ce sun yi hakan ne saboda muhimmancin da matasa ke da shi wajen tafiyar da al'umma.
" Babu wata al'umma da za ta ci gaba ba tare da gudunmawar matasanta ba. Shi ya sa gwamnatinmu ta bawa ci gaban matasa muhimmanci."
- Abba Kabir Yusuf
Sarkin Kano ya kawo shawarar magance daba
A jawabinsa, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yaba da yadda gwamnatin Kano ke gudanar da ayyukan ci gaban al'umma.
Sarkin ya ba iyaye shawarar sanya idanu sosai kan wadanda ke mu'amalantar ƴaƴansu, da yadda suke shige da fice domin saurin kakkaɓe duk wata halayya mara kyau da za su ɗauka, kamar yadda TheGuardian ta ruwaito.
Gwamnatin Kano ta bada umarni kakkaɓe daba
Wasu daga matakan da gwamnatin jihar Kano ta ce tana ɗauka shi ne hana ƴan fim fitar da fina-finan da ke koya daba.
Gwamnatin ta kuma dakatar da masu shirya wasan kwaikwayon daga nuna ƴan daudu a fina-finansu.
Asali: Legit.ng