Gwamnan Kano Ya Yi Jimamin Rasuwar Daso, Ya Mika Sako ga Iyalanta

Gwamnan Kano Ya Yi Jimamin Rasuwar Daso, Ya Mika Sako ga Iyalanta

  • Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana kaduwa bisa rasuwar fitacciyar jarumar fina-finai ta Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso
  • Daso ta rasu ne bayan ta koma bacci jim kadan bayan kammala sahur da niyyar karasa azumi na 30 a watan Ramadan da ya kare jiya
  • Gwamnatin Kano ta hori sauran 'yan Kannywood su yi koyi da halayen Daso na kishin kasa, son zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda ta ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi jimanin rasuwar fitacciyar jarumar shirin fina-finai na Kannywood, Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

Jarumar ta rasu ne cikin baccin ta bayan ta yi sahur da niyyar azumin rana ta 30 a watan Ramadan.

Fitacciyar yar fim din ta rasu da asubahin Talata
Daso ta rasu tana da shekaru 56 Hoto: realsaratudaso
Asali: Facebook

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar, gwamnan ya miƙa ta'azziyyarsa ga iyalan Daso.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Daso ta taka muhimmiyar rawa a shirin fina-finai da ta fito a ciki wanda hakan ya sa ta yi zarra.

Gwamnan ya shawarci sauran ƴan kannywood su yi koyi da halayen Daso na tabbatar da haɗin kan ƴan ƙasa da kishin al'ummarta.

Ya yi addu'ar Allah Ya gafarta mata.

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Saratu Gidado, kamar yadda jaridar Vanguard da Asubahin Talata.

Ƴan uwanta sun ce Daso ta yi mutuwar fuju'a ne bayan ta kwanta bacci jim kaɗan bayan ta yi sahur.

Kara karanta wannan

Fitacciyar jarumar Kannywood Saratu Gidado (Daso) ta rasu

Rahotanni sun ce lafiya ƙalau ta kwanta, amma daga baya aka ga ta rasu.

An binne ta a jihar Kano, inda iyayen ƙasa, ciki har da mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero suka halarci jana'izarta.

Wani jarumin Kannywood ya rasu

Idan za a iya tunawa a shekarar 2023 ma Kannywood ta yi babban rashin jarumi Aminu Mahmud da aka fi sani da Kawu Mala.

Jarumin da ya shahara ta fim mai dogon zango na Dadin Kowa ya rasu bayan fama da ciwon zuciya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel