Okuama: Sojoji Sun Kai Samame Wani Kauye, Sun Kama Mutum 10 da Ake Zargi

Okuama: Sojoji Sun Kai Samame Wani Kauye, Sun Kama Mutum 10 da Ake Zargi

  • Rundunar sojin Najeriya ta kudiri aniyar tsefe ƙaramar hukumar Oghelli da nufin damƙe duk mai hannu a kisan jami'ai a Okuama
  • Wannan ne ya sa dakarun sojojin suka kai samame kauyen Olota kuma suka kama mutum 10 da ake zargi ciki har da shugaban ƙauyen
  • Yayin wannan samame, sojojin sun kwato makamai masu yawa da aka ɓoye a gidan wani mutumi mai suna, Kenneth Okorodudu Atua

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Dakarun sojojin Najeriya da ke aikin bincike sun kai samame wani ƙauye Olota a yankin karamar hukumar Ughelli a jihar Delta ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu.

Wannan samame na zuwa ne biyo bayan kisan sojoji 17 da wasu tsageru suka yi ranar 14 ga watan Maris a garin Okuama da ke ƙaramar hukumar Ughelli.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun halaka ƴan bindiga sama da 150, sun samu nasarori a Arewacin Najeriya

Kauyen Olota.
Okuama: Sojoji sun shiga kauyen Olota, sun kamo waɗanda ake zargi Hoto: @HQNigeriaArmy
Asali: Twitter

An tattaro cewa sojojin sun kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan Okuama baya ga kama shugaban shugaban ƙauyen, Matthew Olokpa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka shiga garin

A cewar wani ganau da ya zanta da jaridar Vanguard, sojojin sun tafi da mutanen da suka kama da kusan dukkan kwale-kwalen mazauna garin da ke ajiye a gefen teku.

Mutumin ya ce:

"Sojoji sama da 200 suka shigo Olota a jirgin ruwa da safiyar nan (jiya), inda suka kama Matthew Olokpa, Bigi Edjekpewhu, German Obiokute, Kenneth Okorodudu Atua, da wasu.
"An riƙa harbe-harben bindiga, sai da muka roki mahukunta su kawo mana ɗauki, su umarci sojojin nan su bar garin nan lami lafiya. Sun tafi da dukkan waɗanda suka kama akalla mutum 10, sun ƙona wasu gidaje.
"Haka kuma sun tafi da kwale-kwale da yawa mallakin mutanen garin. Sai da suka lakaɗa wa shugaban al'umma duka kafin daga bisani su tafi da shi tare da sauran a wani jirgin ruwa na Kenneth."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun dira sansanin manyan ƴan bindiga 3 a Arewa, sun kashe da yawa ranar Sallah

Sunayen waɗanda sojoji suka kama

Wani mazaunin Olota ya shaidawa jaridar Punch sunayen waɗanda sojojin suka kama, sun haɗa da Matthew Olokpa; Bigi Edjekpewhu, German Obiokute, Kenneth da Okorodudu Atuah.

A nata ɓangaren, rundunar sojojin Najeriya ta ce jami'anta sun kwato wani ƙunshi mai ɗauke da bindigu da alburusau a gidan wani mai safarar makamai a Olota.

Rundunar soji ta magantu

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X, rundunar sojojin ta ce an kwato makaman ne daga gidan Kenneth.

Daga cikin makaman da aka kwato daga gidan Kenneth akwai bindigogin G3 guda hudu da magazines, bindigar Pump Action Semi Automatic guda daya, da wasu ƙarin bindigogi da harsashi 476.

Sojoji sun kashe ƴan bindiga

A wani rahoton kuma dakarun sojojin saman Najeriya sun farmaki sansanonin manyan ƴan ta'adda a kananan hukumomi 3 na jihar Zamfara.

Mai magana da yawun NAF, Edward Gabkwet ya ce luguden wutan da jirage suka yi, ya halaka ƴan bindiga masu yawa ranar Sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262