Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri

  • Sabon ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ya kama aiki a ma'aikatar wutar lantarki ta tarayya a Abuja
  • Aliyu a ranar Litinin, 6 ga watan Satumba, ya bayyana cewa shi ba matsafi bane, amma an tura shi ma'aikatar don ƙara ƙima ga abin da ake yi
  • Injiniyan mai shekaru 55 ya maye gurbin Saleh Mamman wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke daga mukaminsa

Sabon Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu ya bukaci 'yan Najeriya da kada su yi tsammanin sihiri a wajen samar da isasshen wutar lantarki, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Aliyu, a lokacin da ya fara aiki a jiya a Abuja, ya ce: "A’a, ni ba matsafi ba ne, amma na zo ne don in kawo ci gaba a abin da ake yi.”

Kara karanta wannan

Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki

Sabon ministan wuta ga 'yan Najeriya: Kada ku yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri
Sabon ministan wuta yace kada 'yan Najeriya su yi tsammanin za a samar da wutan lantarki kamar sihiri Hoto: @hmsfmwhnig
Asali: Facebook

Ya bukaci shugabannin kungiyoyi da hukumomin da ke karkashinsa da su kara kaimi wajen samar da wutar lantarki akai akai ga 'yan kasa.

Ministan ya bukaci ma’aikatan ma’aikatar da su sadaukar da kansu ga aikin da ke gabansu, yana mai nuni da cewa a shirye yake don taimaka musu wajen isar da aikin su, The Cable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya nemi hadin kai domin shi da sauran membobin hukumar su yi nasara, yana mai cewa:

“Ina son kyawawan halayya da gaskiya, kamar yadda ban taba yin karya ba nima ba zan so kowa ya yi min haka ba."

Tun da farko, Babban Sakataren ma’aikatar, Otun Emmanuel, ya sake tunatar da kowa cewa ma’aikata da hukumomin da abin ya shafa suna aiki a matsayin tawaga don isar da aikin Shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar tabbatar da wadataccen wutar lantarki a fadin tarayya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 2 da Shugaban kasa ya duba kafin ya yi waje da Sabo Nanono da Mamman daga ofis

Ya tabbatar wa ministan samun hadin kan su da rubanya kokarinsu don ganin jagorancinsa ya yi kyau.

Dalilin da ya sa Buhari ya miƙa min ma'aikatar lantarki, Sabon Minista, Aliyu

A baya mun ji cewa sabon Ministan Lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tura shi ya karbi ragamar shugabanci a ma'aikatar ne saboda wani dalili na musamman, Daily Trust ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa Aliyu ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki a Ma'aikatar Makamashi a Abuja a ranar Litinin.

Da ya ke bayyana dalilin, Sabon Ministan Makamashin ya ce an turo shi ne domin ya tabbatar an yi komai yadda ya dace a bangaren makamashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng