Kisan Benue – Buhari ya aika sammaci ga Sufeto Janar Idris zuwa Aso Rock
- Shugaba Buhari ya gayyaci Ibrahim Idris zuwa fadar shugaban kasa a Abuja
- A baya shugaban kasar ya nuna bakin ciki akan hare-haren wasu kauyuka a jihar Benue
- Ya ce gwamnati na aiki don tabbatar da cewa an kama masu laifin sannan a hukunta su
A ranar Juma’a, 5 ga watan Junairu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sammaci ga Sufeto Janar nay an sanda Ibrahim Idris a fadar shugaban kasa dake Abuja kan kashe-kashe da akayi kwanan nan a jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bayan wani ganawar sirri shugaban kasar ya bayyana hare-haren a matsayin na cikin gida.
Ya ce ya ba gwamna Sam Ortom tabbacin cewa za’a dauki mataki akan al’amarin domin inganta tsaro a jihar Benue.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun gurfanar da makiyaya 6 da ake zargi da hannu a kisan Benue
Shugaban yan sandan ya kuma kaddamar da cewa babu wani abun tashin hankali sannan kuma cewa akwai tsaro a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng