Fitaccen Malami Ya Saɓawa Sarkin Musulmi, Ya Yi Sallar Idin Ƙaramar Sallah a Sokoto
- Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi sallar iɗin Ƙaramar Sallah a jihar Sakkwato saboda an ga wata a kasar Jamhuriyar Nijar
- Malamin ya bayyana cewa duk wanda ya yi azumi ranar Talata ya saɓawa Sunnah domin an ga wata har a cikin Najeriya
- Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya zauna da kowame malami kan cewa ganin watan ƙasa ɗaya ya isar wa musulman duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Wani fitaccen malamin addinin musulunci a jihar Sakkwato, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya jagorancin idin karamar Sallah a jihar ranar Talata.
A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya bayyana cewa ya aminta da ganin jinjirin watan Shawwal da aka yi a Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, maganar Manzon Allah (SAW) ta tabbata saboda haka azumin watan Ramadan na bana ya ƙare ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa malami Lukuwa ya yi idi?
Da yake bayyana wuraren da aka ga wata da kuma dalilinsa na yin idi yau Talata, Malamin ya ce:
"Maganar Annabi (SAW) ta tabbata, dama cewa ya yi ganin wata ba haihuwarsa ba, ko ka taɓa jin inda Manzon Allah ya faɗi haihuwar wata? Don haka muna da labarin wuraren da aka ga wata har a Najeriya.
"Amma ga binciken da muka yi wanda muka gamsu shi ne na ƙasar Nijar, an ga a wata jihohi shida cikin 8 na Jamhuriyar Nijar, kuma malamai da gwamnati a Nijar sun amince da ganin watan.
"Don haka ba zamu yi azumi ranar Sallah ba domin bidi'a ne, za mu yi wa Manzon allah SAW biyayya domin babu inda ya raba wata ƙasa da wata ƙasa, duniya ta Allah ce, duk inda aka ga wata ya isar ma kowa."
Sheikh Lukuwa ya faɗi hukuncin azumi 30
Dangane da azumin da mafi akasarin ƴan Najeriya suka ɗauka na 30 yau Talata. Sheikh Musa ya ce babu wurin da aka ruwaito Annabi ya yi azumi 30 a rayuwarsa.
Ya kuma bayyana cewa a shirye yake ya yi muƙabala da kowane malami kan ganin wata, inda ya ƙara cewa ba za su tilastawa kowa ya yi Sallah ranar Talata ba.
Idan ba ku manta ba, Sarkin Musulmi ya sanar da cewa ba a ga jinjirin watan Ƙaramar Sallah ba don haka za a cika azumi 30, sallah kuma sai ranar Laraba.
Malami ya warware matsalolin idi
A wani rahoton kuma Sheikh Gidado Abdullahi ya bayyan yadda mutum zai warware matsaloli da suke bijorowa masallata a lokutan sallar idi.
Malamin ya yi bayani akan muhimmancin sallar da kuma dalilan da yasa kowanne musulmi kada yayi sakaci wajen halartar sallar.
Asali: Legit.ng