Innalillahi: Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano Ya Kwanta Dama da Shekaru 59
- An shiga jimami bayan mutuwar ɗan Majalisar dokokin jihar Kano, Halilu Ibrahim Kundila bayan ya sha fama da jinya
- Marigayin Kundila ya rasu ne a daren jiya Asabar 6 ga watan Afrilu ya na da shekaru 59 a duniya kamar yadda aka tabbatar
- Wata majiya daga iyalan marigayin ta tabbatar da mutuwar ɗan Majalisar da ya wakilci mazabar Shanono/Bagwai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Dan majalisar jihar Kano, Halilu Kundila ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 59 a duniya.
Marigayin wanda ɗan jami'yyar APC ne ya rasu a jiya Asabar 6 ga watan Afrilu, kamar yadda Punch ta tattaro.
Yaushe aka gudanar da sallar jana'izarsa?
Kundila wanda ya wakilci mazabar Shanono/Bagwai ya rasu ne a daren ranar Asabar 6 ga watan Afrilu bayan ya sha fama da jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga iyalansa ta tabbatar da cewa an gudanar da sallar jana'izarsa a yau Lahadi 7 ga watan Afrilu a Kundila da ke karamar hukumar Shonono.
"Dan Majalisar ya rasu ne a daren jiya Asabar 6 ga watan Afrilu bayan 'yar gajeruwar jinya an kuma binne shi a garin Kundila."
- Cewar majiyar
Daga cikin wadanda suka halarci jana'izarsa akwai dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Shanono/Bagwai, Yusuf Badau da sauran mambobin Majalisar dokokin jihar.
Marigayi Halilu Kundila ya rasu ya bar mata har guda hudu da kuma 'ya'ya guda 17 a duniya, cewar Daily Post.
Kafin rasuwar marigayin ya raba kayan tallafi a makon da ya gabata domin saukakawa 'yan yankinsa.
Babban manaja a hukumar NIWA ya rasu
A baya, mun ruwaito muku cewa Babban manajan hulda da jama'a a hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Tarayya (NIWA), Dardau Jibril ya riga mu gidan gaskiya.
Dardau ya rasu ne da safiyar ranar Juma'a 5 ga watan Afrilu jim kadan bayan jagorantar sallar asuba a birnin Lokoja da ke jihar Kogi.
Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa bayan kammala sallar Juma'a tare da binne shi a makabartar unguwar Power da ke Lokoja kamar yadda aka sanar tun farko.
Asali: Legit.ng