InnalilLahi: Manaja a Hukumar NIWA Ya Rasu Jim Kadan Bayan Jagorantar Sallar Asuba

InnalilLahi: Manaja a Hukumar NIWA Ya Rasu Jim Kadan Bayan Jagorantar Sallar Asuba

  • An shiga jimami bayan manaja a Hukumar kula da hanyoyin ruwa (NIWA) ya rasu da safiyar yau Juma'a a jihar Kogi
  • Marigayin Dardau Jibril ya rasu ne jim kadan bayan jagorantar sallar asuba a masallaci da ke birnin Lokoja a jihar
  • Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwar Dardau inda su ka ce za a binne a makabartar unguwar Power da ke birnin Lokoja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Babban manajan hulda da jama'a a hukumar kula da hanyoyin ruwa ta Tarayya (NIWA), Dardau Jibril ya riga mu gidan gaskiya.

Dardau ya rasu ne da safiyar yau Juma'a 5 ga watan Afrilu a birnin Lokoja da ke jihar Kogi, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Neja: 'Yan bindiga sun kai hari kan masu ibada a lokacin sallar Tahajjud

Babbar ma'aikacin hukumar NIWA ya kwanta dama bayan sallar asuba
Manajan hulda da jama'a a Hukumar NIWA, Dardau Jibril ya rasu. Hoto: Dardau Jibril.
Asali: Facebook

Yadda marigayin ya rasu bayan sallar asuba

Iyalan marigayin sun tabbatar da cewa Dardau ya rasu ne jim kadan bayan ya gama jan sallar asuba a masallaci a Lokaja da ke jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dardau Jibril ya rasu ne bayan ya gama jan sallar asuba yau Juma'a 26 ga watan Ramadan wanda ya zo dai-dai da 5 ga watan Afrilun 2024."
"Za a birne shi a makabartar unguwar Power da ke Lokoja bayan sallar Juma'a a yau."

- Iyalan marigayin

Yadda Dardau ke hidimar addini

Dardau ya rike manaja a hukumar ne bayan tsohon manaja, Tayo Fadile ya yi ritaya daga aiki, kamar yadda Daily Trend ta tattaro.

Dardau ya kasance mutum mai hidimar addini sosai ga wanda ya ba da gudunmawa sosai wurin inganta harkokin addinin Musulunci a rasuwarsa.

Tuni aka gudanar da sallar jana'izarsa bayan kammala sallar Juma'a a yau tare da binne shi a makabartar unguwar Power da ke Lokoja kamar yadda aka sanar tun farko.

Kara karanta wannan

Masallata sun sha da kyar a sallar tahajjud, mota ta kutsa masallaci a jihar Arewa

Tsohon shugaban NLC, Ali Chiroma ya rasu

A baya, kun ji labarin cewa tsohon shugaban kungiyar NLC, Ali Chiroma ya riga mu gidan gaskiya.

Chiroma ya rasu ne a ranar Talata 2 ga watan Afrilu a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri a jihar Borno.

Bayan rasuwar, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon jaje inda ya bayyana marigayin a matsayin shugaba kuma mutun marar tsoro a rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel