Fatawa a Kan Fitar da Kudi a Matsayin Zakatul Fitr Daga Sheikh Jamilu Zarewa

Fatawa a Kan Fitar da Kudi a Matsayin Zakatul Fitr Daga Sheikh Jamilu Zarewa

Kaduna - Dr. Jamilu Yusuf Zarewa babban malamin addinin musulunci, tun 2018 ya amsa tambaye game da abin da ya shafi Zakatul-Fitr.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Legit ta dauko tambayar da aka yi wa wannan shehin malami da amsar da ya ba da daga fatawar wasu manyan malaman duniya da aka yi.

Zakatul fitr
Ana yin Zakatul fitr a karshen Ramadan Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana ba da zakkar nan ne a karshen watan Ramadan domin a yi bikin karamar sallah.

Zakatul-fitr: Kudi ko kayan abinci?

Tambaya:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Assalamu alaikum Dr. Shin ana iya bada kuɗi a Zakatul-fitr maimakon kayan abinci?

Amsa:

Wa alaikum assalam. Annabi (S.A.W.) ya wajabta Zakkar fidda sa'i na dabino ko Sha'ir, kamar yadda ya zo a Hadisin Ibnu Umar wanda Muslim ya rawaito a lamba ta: (2287).

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

Abin da Malamai suka fahimta a Hadisin da ya gabata shi ne ana fitar da Zakkar fid-dakai ne daga abin da mutanen garinku suka fi ci kamar Shinkafa, Dawa, Masara, a wajan ƴan Nigeria.

Fuƙaha'u sun yi saɓani game da bada kuɗi a maimakon abincin da ya zo a Hadisi:

Ra’ayi na farko game da zakatul-fitr

Umar ɗan Abdulaziz da Abu-Hanifa da Ibnu-Taimiyya da Albani da wasu magabata sun tafi akan halaccin bada kuɗi a maimakon Zakkar fid-da kai, saboda abin da ya sa aka shar'anta Zakkar fid-dakai shi ne: wadatar da talakawa daga barin roƙo a ranar Idi, hakan kuma yana tabbata ta hanyar bada kuɗi ko ƙimar abincin.

Ra’ayi na biyu game da zakatul-fitr

Ya wajaba a fitar da abincin da mafi rinjaye suke ci, saboda tun da Annabi (S.A.W.) ya faɗi sunayen abinci, hakan sai ya nuna su yake so a fitar ba ƙimarsu ba, kamar yadda yake a Hadisin Ibnu Umar wanda ya gabata.

Kara karanta wannan

Jerin ƙasashen Afirka 12 da tarin basussuka ya masu katutu kuma ya zama barazana

Menene ya fi dacewa a Zakatul Fitr?

Zance na biyu ya fi inganci, saboda bin Sunnar Manzo SAW shi ne daidai, tare da cewa idan an samu lalura ta ƙarancin abinci ko kuma talakawa suka nuna sun fi buƙatar kuɗi, ya halatta a fitar da kuɗin ko ƙimar abincin a maimakonsa, saboda akwai Hadisai da suke nuna halaccin amsar ƙima a babin Zakkar dabbobi idan Sa'i bai samu dabbar da ya kamata ya amsa ba.

Manazarta da madogara

Al-mabsud 2/156, da kuma Al'istizkaar 9/346, da Al'iktiyarat Alfiƙhiyya lil'Albani na Abu-shaɗy, shafi na 209-210.

Allah ne mafi sani.

13/7/2018

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Kirista ya ji dadin karanta Kur'ani

A kwanaki an ji labari Kiristan ‘dan wasan fim, Will Smith ya karance Kur’ani daga Baqarah zuwa Nas a watan azumi watau Ramadan.

Tauraron Amurkan ya ce ya yi mamakin yadda ya samu littafi mai tsarki da saukin fahimta, ya kuma yi mamakin ambaton Annabi Musa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng