Zakkar Fitar-da-kai na cike ladan Azumin Ramadan
- Zakkar Fitar-da-kai na cike ladan Azumin Ramadan
– Yau, Asabar 2 ga watan Yuli za a kai Azumi na 27
– Ana tattaunawa a duniyar musulunci game da Zakatul Fitr
Zakatul Fitr dai an fi sanin sa da Zakkar Fitar da kai a Kasar Hausa, ana kiran sa ‘JAKA’ a Kasar Yarabawa. Sadaka ce da ake badawa cikin karshen watan Ramadan, ana bada hatsi ga musulman da suka yi Azumin watan Ramadan kuma ba su da halin buda baki yayin bikin Sallah.
Ga yadda ake ba da wannan Zakkah Idan Azumin Ramadan ya zo Karshe, ana bada wannan sadaka ga musulman da suka azamci Ramadan, amma ba sa da halin buda baki. Ana ba da abin da suka shafi; Shinkafa, gero, dawo, acca, alkama da sauran su dai na game da hatsi.
Mudu
Mudu wani dan kofi ne da ake auna hatsin da za a bada sadaka. Ana bada mudu guda 4 ga kowane iyali da ke karkashin mutum. Misali mai gida yana da iyali da suka hada da: mata 2, ‘ya ‘ya 9, masu aiki 2, kannai 2, da kuma yaron sa 1, zai bada mudu 68 kenan. (Idan aka yi lissafi za a ga mutane 17, har da maigidan. To a lissafa 17 dinnan sau 4, shi zai bada 68). Idan an rasa mudu sai ayi amfani da wani makamancin san a awo.
Zakatul Fitr na da lada a wajen Allah mai girma.
Hujjar Zakar Fitar da kai daga Hadisan Manzon Allah.
Abdullahi dan Umar (Allah ya yarda su) ya ruwaito cewa Manzon Allah (Allah kara masa tsira) yace: “Zakatul Fitr dole ne akan kowane baligi musulmi” Bukhari da Muslim sun ruwaito wannan hadisi.
Malamai sun ce ana bada hatsi; dawa, gero, shinkafa, acca, alkama ne, musamman wanda aka fi ci a yankin da mutum yake. Zakatul Fitr dai yana taimakawa musulmai wadanda ba su da hali su sami abin da za su ci, su sha lokacin bikin karamar Sallah. Ana kuma bada wannan zakkan kai ne kafin a dawo daga masallacin idi. Haka wasu malamai suna ganin ya halarta a bada kudi a maimakon sadakan, sai dai mafi yawan malamai, suna ganin cewa bai halarta ba a bada kudi a maimakon hatsin.
Asali: Legit.ng