Will Smith Ya Fadi Abin da Ya Ba Shi Mamaki a Matsayin Kirista da Ya ‘Sauke’ Kur’ani

Will Smith Ya Fadi Abin da Ya Ba Shi Mamaki a Matsayin Kirista da Ya ‘Sauke’ Kur’ani

  • Will Smith ya komawa addini domin samun mafitar mawuyacin halin da ya tsinci kan shi a ‘yan shekarun nan
  • ‘Dan wasan kwaikwayon ya shaida cewa ya karanta Kur’ani gaba daya a azumin Ramadan na shekarar bara
  • Tauraron ba musulmi ba ne, amma ya yi sha’awar yadda ya ga zubin Kur’anin da musulmai suke amfani da shi
  • Tun a Disamban shekarar bara aka yi hira da fitaccen 'dan wasan, kuma hakan bai nufin ya canza addininsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

U. S - Fitaccen tauraron Hollywood, Will Smith, ya shaida cewa ya karanta Al-Kur’ani wanda shi ne Littafi mafi tsarki ga Musulmai.

‘Dan wasan kwaikwayon ya yi ikirarin karanta daukacin Al-Kur’ani da Musulman duniya suka yi azumin shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Shahararren mawaki a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya a yau Juma'a

Will Smith
Kur'ani ya ba 'dan wasan Amurka Will Smith da azumi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Will Smith ya karanta Al-Kur'ani da azumi

Will Smith ya bayyana wannan a lokacin da fitaccen ‘dan jaridar nan na kasar Masar, Amr Adeeb ya yi hira da shi a wani shirin Podcast.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tauraron mai shekaru 55 a duniya ya ce bayan Kur’ani, ya kuma karanta wasu littatafai masu tsarki kamar At Taura da kuma Injila.

Saukin Kur'ani ya burge Will Smith

Amma a cikin wadannan Littatafai da Musulmai, Kiristoci da Yahudawa suka runguma, Smith ya ce Al-Kur’ani ne ya fi burge shi.

Abin da ya fi ba ‘dan wasan sha’awa kamar yadda Hindustan Times ta rahoto shi ne ganin yadda ma’anonin Liitafi mai tsarkin ya fito fili.

“Ina kaunar saukinsa. A fili Al-Kur’ani yake. Da wahala ka samu wani rashim fahimta a cikinSa."
"Ka san a cikin shekaru biyu da suka wuce, na shiga mawuyacin hali, sai na komawa ruhi na."

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da Musulmi ya kamata ya fi ba kulawa a watan Ramadan

- Will Smith

Kur'ani: Abin mamakin da Will Smith ya gani

A lokacin da yake karatun Al-Kur’ani, an ji Will Smith a X yana cewa babu abin da ya ba shi mamaki kamar ambaton Annabi Musa.

Wannan ne karon farko da tauraron ya ji wannan, sai ya ji tamkar an dauko labarin Annabin ne daga cikin At-Taura ko kuwa Injila.

Gwamna ya je wajen rabon abincin azumi

Rahoto ya zo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci inda ake raba abinci ga mabuƙata a jihar Kano a watan azumin Ramadan.

Mai girma Gwamnan bai gamsu da abin da ya tarar a wajen rabon abincin ba, an ji shi ya fusata bayan ware makudan kudi ga shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel