Zakkar Fidda-Kai da yadda ake fidda ta a Musulunci

Zakkar Fidda-Kai da yadda ake fidda ta a Musulunci

Idan Azumi ya kai dab da karshe, akwai Zakkar abinci da ake bayarwa don dada samun lada a wurin Allah da kuma kankare zunubban da suka yi saura na miyagun maganganu da makamantansu, shi ya sa ma ake kiranta da sunan “Zkkar fidda-kai”

HUKUNCIN ZAKKAR FIDDA-KAI:

Bayar da wannan Zakkar wajibi (farilla) ne, kamar yadda Hadisin Abdullahi Dan Umar (RA) ya nuna. (Riwayar Bukhari da Muslim)

Kuma ta na wajaba ne a kan ‘da, ko bawa namiji ko mace, babba ko yaro, matukar dai musulmi ne wanda ya mallaki abincin wuni daya, na sa da na iyalansa, ba sai wanda ya mallaki dukiya mai yawa ba.

Zakkar Fidda-Kai da yadda ake fidda ta a Musulunci
Zakkar Fidda-Kai da yadda ake fidda ta a Musulunci

Abdullahi Dan Abbas (RA) yace: “M anzon Allah (SAW) ya farlanta zakkar fidda kai, tsarkakewa ne ga mai azumi, daga maganganun da ba su dace ba, kuma abinci ne ga miskinai” (Riwayar Abu Dauda, Ibnu Maja).

Abdullahi Dan Umar (RA) kuma cewa ya yi: “Manzon Allah ya yi umurni da zakkan fidda-kai ga yaro da babba, ‘da bawa, daga wadanda kuke kula da su” (Riwayar Daru Kudniy) .

Don haka mai gida mai hali zai ba da nasa da na iyalansa da kuma yaransa gaba daya wadanda dai suke karkashinsa, Sun yi azumi ne ko ba su yi ba, don faranta ran talakawa da miskinai ranar sallah kada su je bara ko roko, ana cikin farin ciki su kuma suna bakin ciki, shi ya sa aka ce a ba su don a faranta mu su rai.

ABIN DA ZA A BAYAR:

Za a bayar da Sa’i guda ne na kowane mutum daga dukkan nau’in abin da ake kiransa abinci, ba lallai sai dabino ko Sha’ir ko Alkama ba, wannan shi ne bayanin da malamai suka tabbatar.

Don haka za a iya bayar da sa’in dawa, gero, masara, shinkafa da garin hatsi, ko na kwaki, matukar dai abinci ne babu laifi.

[Dun karin bayani duba Sifatu Saumin Nabiyyi (SAW) Akwai Malaman da suke ganin in har akwai bukatar a bayar da

kima, ko kudi, ana iya bayarwa, amma a bayar da abin da shi ya fi.

KARIN BAYANI:

Sa’i shi ne Muddin Nabiyyi guda hudu, cikin tafukan hannun matsakaicin mutum a hade shi ne Muddin Nabiyyi.

LOKACIN FITARWA:

Ana bayar da wannan Zakkar ne ana gobe sallah kafin a fita zuwa Masallaci, kamar yadda Hadisin ‘Dan Umar (RA) ya nuna cewa “Manzon Allah ya yi umarni da bayar da zakkan fidda-kai kafin fitan mutane zuwa masallaci” (Bukhari da Muslim).

Amma ya halatta a bayar kwana daya ko biyu kafin sallah, saboda maganan Nafi’u (RA) da ya yi na cewa “Abdullahi dan Umar ya kasance yana ba da wadanda suke karban, sun kasance an aba su ne kuwa kafin ranar sallah da kwana daya ko biyu” (Bukhari da Muslim).

Don haka ni ina ganin bayarwa kafin kwana ‘daya ko biyu shi ya fi, don mutane su samu daman sarrafa abin da aka ba su, sai dai idan Zakkar da shinkafa ce ko gari, wannan kam ba ya bukatar wata wahala, ko ranar sallah ana iya bayarwa.

WANDA ZA A BA WA

Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai ya bayar don ya samu wadatuwa.

Kuma lallai ne a bayar da zakkar kafin a tafi masallacin Idi, don Annabi (SAW) ya ce: “Duk wanda ya bayar kafin aje sallah, zakka ce karbabbiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma sadaka ce cikin sadakoki kawai”.(Riwayar Abu Dawud da Ibnu Majah).

Don haka sai a yi kokari a bayar da wuri don a kwantar wa miskinai da hankali, a sanya musu farin ciki da walwala, a kuma rufa mu su asirinsu, don su ji dadin shagulgulan Idi tare da iyalansu da abokansu da ‘yan uwansu.

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Sababbin Jam'iyyu za su kawo mafita a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel