NERC Ta Tsokano Yan Kwadago, Ana Yi wa Tinubu Barazana Saboda Kudin Lantarki

NERC Ta Tsokano Yan Kwadago, Ana Yi wa Tinubu Barazana Saboda Kudin Lantarki

  • Kungiyoyin kwadago ba su yi na’am da yadda hukumar NERC ta ba kamfanonin DisCos damar tashin kudin lantarki ba
  • Wani shugaba a NLC ya zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da biyewa bankin duniya da masanan da ke aiki a IMF
  • Shugaban AECPF ya yi ikirarin karin kudin lantarki ya saba ka’ida, ya yi barazanar zanga-zanga da yin kara a kotu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyoyin kwadago sun fito sun nuna rashin amincewarsu da karin kudin wutar lantarki da aka yi wa wasu a kasar nan.

Matakin da gwamnatin tarayya ta dauka bai yi wa ma’aikata dadi ba, kungiyoyi suna zargin ana biyewa irinsu IMF da bankin Duniya.

Kara karanta wannan

Ba a haka: Atiku ya taimakawa Tinubu da shawarwari kan karin kudin wutar lantarki

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
‘Yan kwadago sun soki tashin kudin lantarki a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mecece matsayar NLC kan kudin lantarki?

Shugaban sashen yada labarai na kungiyar NLC, Benson Upah ya shaidawa Punch babu tausayi a sabon tsarin da aka fito da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan gwamnati mai-ci ta dage farashin kudin lantarki zai tashi da kusan 300%, kungiyar kwadago ta ce a shirya abin da zai biyo baya.

Kwamred Benson Upah yake cewa ‘yan kasuwa suna kukan cewa tsadar wuta zai taba aikinsu, hakan kuma zai shafi farashin kaya.

"Abin ya ba mu mamaki a ji Minista yana karfin hali yana cewa za a cigaba da tsarin.
Hakan ya nuna ba shugaban kasa da ministan ke rike da kasa ba. Mutanen bankin Duniya da IMF suke jan ragamar mugun tsarin nan."

-Benson Upah

Business Day ta ce ‘yan kwadago sun bukaci a cigaba da saida lantarki a farashin da aka sani, ba su goyon bayan a janye tallafi a wuta.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ce za ta kuma kara kudin wutar lantarki, ta fadi dalili

Zanga-zanga ko sauke farashin lantarki

Shugabannin kungiyar AECPF sun ba hukumar NERC ta kasa wa’adin sa’o’i 72 ta janye wannan kari da aka yi wa ‘yan sahun farko.

Jaridar Leadership ta ce idan ba a biyawa AECPF bukata ba, za a shigar da karar NERC a kotu, sannan za a barke da yin zanga-zanga.

Shugaban kungiyar ta kasa, Adeola Samuel – Ilori ya shaida cewa karin kudin da aka yi ya sabawa doka, kuma ba za su yarda da shi ba.

Atiku ya soki tashin kudin lantarki

A rahoton da aka fitar a baya, an ji karin kudin wutar lantarki ya jawo Atiku Abubakar ya dauki zafi a kan Gwamnatin Bola Tinubu.

Atiku Abubakar ya ce gwamnatin tarayya tana harbin iska ne, ya kawo muhimman shawarwarin yadda yake ganin za a inganta lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel