Gwamnati Ta Ci Kamfanin AEDC Tarar N200m Saboda Zaluntar Mutane Wajen Shan Lantarki

Gwamnati Ta Ci Kamfanin AEDC Tarar N200m Saboda Zaluntar Mutane Wajen Shan Lantarki

  • AEDC ya rika saida lantarki ga duka abokan hulda da cinikinsa a kan sabon farashin da aka amincewa ‘yan sahun farko
  • Hukumar NERC ta dauki mataki a kan kamfanin raba wutan na Abuja, zai biya tarar Naira miliyan 200 saboda saba umarni
  • Kamfanin zai kuma maidawa wadanda suka saye wuta kudi a farashin da ba na su ba, kamar yadda sanarwar ta tabbatar

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar NERC ta fitar da sanarwa cewa an hukunta kamfanin AEDC saboda saba umarnin da aka ba da a kan kudin lantarki.

A makon nan NERC ta amince a kara farashin wutar lantarki ga wadanda suke sahun farko, matakin da Atiku Abubakar ya soka.

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Kamfanin Lantarki Energize, AEDC
AEDC v NERC: An ci tarar kamfanin lantarki N200m a Abuja Hoto: www.abujaelectricity.com, Energize
Asali: UGC

NERC ta yabawa AEDC tarar N200m

Sanarwar da hukumar kula da harkokin wutar lantarkin ta fitar a shafinta na X a jiya ya nuna an samu AEDC da laifin sabawa umarni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin da ke rabon wutar lantarki a birnin Abuja da kewaye zai biya N200, 000, 000 a dalilin yin coge wajen kasa masu shan wuta.

Lantarki: Laifin da kamfanin AEDC ya aikata

Karin da aka yi ya shafi ‘yan sahun farko ne kurum wadanda ake ikirarin suna shafe akalla awanni 20 da hasken wuta a kowace rana.

A gefe guda kuwa sai kamfanin AEDC ya yi wa kowa kudin goro, ya rika saida wuta a kan farashin da NERC ta ce a saidawa daidaiku.

Saboda haka kamfanin rabon wutan zai biya 200,000,000.00 a matsayin tara. Abin da ba a sani ba shi ne ko AEDC zai iya neman sauki.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ce za ta kuma kara kudin wutar lantarki, ta fadi dalili

AEDC zai maidawa mutane kudin lantarki

Hukumar ta ba kamfanin na AEDC umarnin dawowa duk wanda aka saida masa wuta da sabon farashi alhali bai cikin sahun Band A.

A karshen sanarwar da aka fitar a dandalin, hukumar NERC ta ce da gaske ta ke yi wajen kare abokan huldar kamfanonin lantarki.

NERC ta na kokari wajen tabbatar da ana yin abin da ya dace a harkar wutar lantarki.

NLC ta soki tsadar wutar lantarki

Ana da labarin yadda NLC ta soki Ministan tarayya saboda ya ce idan dai batun karin kudin lantarki ne yanzu aka fara a Najeriya.

‘Yan kwadago sun ce Bankin duniya da IMF ne suke juya shugaban kasa da ministan harkar wuta, sun yi barazanar yin zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng