Masallata Sun Sha da Kyar a Sallar Tahajjud, Mota Ta Kutsa Masallaci a Jihar Arewa
- An shiga fargaba bayan wata babbar mota ta kauce hanya tare da kutsawa cikin masallaci bayan idar sallah a jihar Neja
- Direban motar ya gagara shawo kan motar ce bayan bacci ya dauke shi inda ya rusa wani bangare na masallacin a jihar
- Mazauna yankin sun tabbatar da lamarin ya faru ne da asubahin yau Juma’a 5 ga watan Afrilu jim kadan bayan idar da salla
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Neja – Wata babbar mota dauke da mangwaro ta kutsa cikin masallaci jim kadan bayan an idar da sallar tahajjud a jihar Neja bayan direban motar ya fara barci.
Lamarin ya faru ne asubahin yau Juma’a 5 ga watan Afrilu kusa da tsohon ofishin Lasisi a Kontagora da ke jihar.
Yadda lamarin ya faru bayan idar da salla
Daily Trust ta ruwaito cewa masallata sun watse kenan bayan halartar sallar tahajjud bai wuce da mintuna ba lokacin da lamarin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masallacin ya cika da masallata yayin al’ummar Musulmi ke neman falala a kwanaki 10 na karshen watan Ramadan.
Bangaren masallacin da abin ya shafa wurin mata ne da yara wadanda suka halarci sallar tahajjud.
Wata majiya ta tabbatar da cewa direban motar ya fito ne daga Bida inda ya ke kokarin wucewa jihar Sokoto da fasonjoji guda hudu.
Martanin wani mazaunin yankin
Wani mazaunin yankin, Yahaya Sulaiman ya ce lamarin ya faru ne mintuna shida bayan mutane sun waste daga masallacin.
“Mun godewa Allah, wurin da motar ta buga bangaren mata ne da yara, kuma mutane sun watse kenan kafin lamarin ya faru.”
“Babu rasa rai ko guda daya dalilin hatsarin amma sai dai wani bangare na masallacin ya lalace.”
- Yahaya Suleiman
Daya daga cikin fasinjojin, Mustapha Sokoto ya ce ya na cikin barci kawai ya tsinci kansa a kasa, a cewar Vanguard.
‘Yan bindiga sun hallaka sabon ango
A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun yi ajalin wani sabon mai suna Sani a garin Madaka da ke karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Marigayin wanda aka tabbatar mahauci ne da ke zaune a garin Kagara ya rasa ransa ne bayan ya je kasuwa siyo nama.
Asali: Legit.ng