Ramadan: Musulmai fiye da miliyan 2 suka yi sallar Tahajjud a daren 27 a Saudi Arabiya

Ramadan: Musulmai fiye da miliyan 2 suka yi sallar Tahajjud a daren 27 a Saudi Arabiya

  • Sama da mutum miliyan biyu suka tsaya wajen sallar daren da aka yi a ranar 26 ga watan Ramadan
  • Dinbin mutane sun halarci sallar tahajjud a daren na 27 da sa ran dacewa da albarkar Laylatul Kadari
  • Musulmai su na yin ibada na musamman a goma karshen watan Ramadan a ko ina a fadin Duniya

Saudi - Fiye da mutane miliyan biyu suka halarci sallar tsayuwar dare da aka yi a masallacin Makkah a daren 27 ga watan Ramadan na shekarar 1443.

Kamar yadda sanarwa ta fito daga hukumar da ke kula da masallatan kasa mai tsarki na Saudi Arabia a Twitter, dinbin mutane suka yi ibada a daren jiya.

Maniyyata da sauran masu ibada a cikin watan azumi su kan yi sallar dare a Masjid Al Haram watau masallaci mai tsarki da yake garin Makkah a Saudi.

Kara karanta wannan

Eid al Fitr: Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da ranar da za fara duban jinjirin watan sallah

Sanarwar ta ce a daren 27 ga watan nan mai alfarma, masallacin ya cika sosai, ya tumbatsa.

A addinin musulunci babu daren da suka kai na watan Ramadan daraja. A cikin dararen kuma, ana fifita wadanda suka fado a cikin goma na karshen watan.

Har ila yau, ana bada muhimmanci ga dararen mara watau na 21, 23, 25, 27, 29. Daren 27 da aka cika masallacin, ya na cikin wadannan darare a musulunci.

Saudi Arabiya
Masu ibada a masallacin Ka'aba Hoto: @hsharifain
Asali: Twitter

Malaman addinin musulunci su na kyautata zaton a irin wannan lokaci a dace da Laylatul Qadr watau daren da darajarsa ta zarce ta kowane dare a Duniya.

Kamar yadda shafin Haramain Sharifain suka bayyana, Sheikh Abdul Rehman Al Sudais da Maher Al Mu’aiqly su ka yi limancin sallar cikin tsakar daren.

Kara karanta wannan

Daren Lailatul Kadri: Aisha Buhari ta yiwa mutanen Zamfara addu’a ta musamman

Sheikh Salah Al Budayr shi ne limamin da ya gabatar da addu’o'i na musamman a sallar daren da aka gudanar a masallacin Annabi (SAW) da ke birnin Madina.

Gwamnati ta yi tanadi

Dama can gwamnatin kasar Saudi ta yi shiri na musamman a kwanakin karshe na Ramadan saboda ana sa ran yawan masu zuwa yin ibada zai karu sosai.

Wai jami’in gwamnatin kasar, Hamad bin Faihan ya shaidawa jaridar Arab News cewa akwai ma’aikata 18, 000 da aka ware saboda kula da masu aikin Umrah.

Limami ya rasu a tahajjud

A lokacin da Musulmai ke Azumin Ramadan, kuma aka shigo goman karshe, sai aka ji labarin mutuwar wani Limami ya na Tahajjud a garin Zaria, jihar Kaduna.

Malam Muhammad Sani Lawan ya rasu ne bayan ya yi sujuda ga Allah, ya na mai limancin sallar tsakar dare a cikin daren 23 ga watan Ramadan na shekarar nan.

Kara karanta wannan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi ya biya N16m, ya ceto Bayin Allah daga kurkuku a Ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel