Jerin Jihohi 10 na Najeriya da Ke da Yawan Basussukan Waje a Wuyansu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ofishin kula da basussukan Najeriya (DMO) ya bayyana jimillar basussukan waje na jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
A bayanan da DMO ya fitar basussukan waje da aka biyo jihihon ƙasar nan da birnin tarayya Abuja, ya kai dala biliyan 4.61 a ranar 31 ga watan Disamba, 2023.
Wannan ya nuna cewa an samu ƙari daga kan dala biliyan 4.46 da aka samu a shekarar 2022.
A cikin shekara guda, bashin waje na jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ya ƙaru da kusan kaso 3.36% ko kuma dala miliyan 150.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Nairametrics ta jero jihohi 10 na Najeriya da suka fi yawan bashin ƙasashen waje a kansu.
Jihohi masu bashin waje mafi yawa
Ga jerinsu nan ƙasa:
1. Jihar Legas
Jihar Legas na kan gaba cikin jerin jihohin Najeriya da ke da yawan basussuka a kansu.
Bashin waje da ake bin jihar ya kai dala biliyan 1.24 a shekarar 2023. Sai dai, wannan adadin bai kai bashin dala biliyan 1.25 da jihar ta ciyo ba a shekarar 2022.
An samu wannan ragin ne saboda dogaro da ƙarin bashin cikin gida wanda ya kai kimanin naira tiriliyan 1.05, ƙididdigar DMO ta tabbatar.
2. Jihar Kaduna
Jihar Kaduna na da bashin waje a kanta na dala miliyan 587.07 a shekarar 2023, wanda ya haura daga dala miliyan 573.74 a shekarar 2022.
3. Jihar Edo
Basussukan waje na jihar Edo sun haura zuwa dala miliyan 314.45 a shekarar 2023 daga dala miliyan 261.15 a shekarar 2022.
4. Jihar Cross River
Basussukan wajen jihar Kuros Ribas sun ƙaru zuwa dala miliyan 211.13 a shekarar 2023 daga dala miliyan 209.53 a shekarar 2022.
5. Jihar Bauchi
Da bashin wajen dala miliyan 187.63 a shekarar 2023, jihar Bauchi ta samu ƙari daga dala miliyan 165.78 a shekarar 2022.
Ƙaruwar basussukan na nuna buƙatar ƙara samar da hanyoyin samun kuɗaden shiga.
6. Jihar Ogun
Adadin bashin waje da ke kan Jihar Ogun da ke makwabtaka da Legas ya kai dala miliyan 168.83 a shekarar 2023, inda ya ƙaru daga dala miliyan 136.26 a shekarar 2022.
7. Jihar Ekiti
Basussukan waje da ake bin jihar Ekiti ya ƙaru sosai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. A shekarar 2022 bashin waje da aka biyo jihar ya kai dala miliyan 105.59, sai dai wannan adadin ya ƙaru zuwa dala miliyan 121.05 a cikin shekarar 2023.
8. Jihar Enugu
Jihar Enugu ta samu raguwar basussukan waje da aka biyo ta. Basussukan sun ragu daga dala miliyan 120.86 a shekarar 2022 zuwa dala miliyan 120.45 a shekarar 2023.
9. Jihar Kano
Basusukan waje da ake bin jihar Kano ya ƙaru zuwa dala miliyan 107.92 a shekarar 2023, sama da dala miliyan 100.67 a shekarar 2022. Hakan ya nuna an samu ƙaruwar kaso 7.2%.
10. Jihar Anambra
Jihar Anambra ita ce ta zo ta 10 a cikin jerin jihohin da basussukan waje da aka biyo su ke da yawa.
A shekarar 2023 bashin waje da aka biyo jihar ya kai dala miliyan 107.24, wanda hakan ke nuna samun ƙari daga dala miliyan 103.82 a shekarar 2022.
Bashin waje na Najeriya ya ƙaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa bashin da ƙasashen Faransa, China, Indiya, Jamus da Japan ke bin Najeriya ya ƙaru sosai.
Ƙididdigar da ofishin kula da basussukan Najeriya (DMO) ya fitar ta nuna aƙalla ƙasashen biyar na bin Najeriya dala biliyan 5.
Asali: Legit.ng