Jerin Kasashe 5 da Ma'aikata Ke Samun Mafi Karancin Albashi a Duniya
- Ma'aikata a Najeriya na daga cikin waɗanda ake biyansu albashi mara tsoka a faɗin duniya duk da kiraye-kirayen da ake yi na a yi musu ƙari
- Najeriya ce ƙasa ɗaya tilo daga yankin Afirika ta Yamma da ta shiga cikin jerin ƙasashe masu mafi ƙarancin albashi a duniya
- Sauran ƙasashe huɗu da ke cikin jerin ƙasashen da ma'aikata ba su mori albashi mai kyau ba duk sun fito ne daga yankin Asiya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) na ci gaba da yin kira da a ƙara wa ma'aikatan ƙasar nan mafi ƙarancin albashi, saboda tabarbarewar tattalin arzikin da ake fuskanta.
Mafi ƙarancin albashin ma'aikata a duniya lamari ne mai muhimmanci da gwamnati ta maida hankali a kai domin kula da ma'aikata.
Kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito, masana tattalin arziki da yawa na kallon mafi ƙarancin albashi a matsayin abu mai muhimmanci ga masu ɗaukar aiki da ma'aikata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙasashe 5 masu mafi ƙarancin albashi
Ga jerin ƙasashe biyar da ke da mafi ƙarancin albashi:
1. Najeriya
Mafi ƙarancin albashin Najeriya ₦30,000 ($77) duk wata, ya zama ɗaya daga cikin mafi ƙarancin albashi a duniya.
Najeriya ita ce ƙasa ɗaya tilo a yankin Afirika ta Yamma da ta shigo cikin jerin sunayen.
2. Bangladesh
Ƙasar Bangladesh na daga cikin ƙasashe mafi ƙarancin albashi a yankin Asiya.
An ba da rahoton cewa ma'aikatan Bangladesh a ɓangaren masana'antar sutura suna samun kusan Dala 95 a kowane wata.
3. Fakistan
Ƙasa ta biyar mafi yawan jama'a a duniya, wacce ke da yawan mutane sama da miliyan 241.5 tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu mafi ƙarancin albashi a duniya.
Matsakaicin mafi ƙarancin albashi a ƙasar ta yankin Kudancin Asiya ya danganta da lardin da ma'aikaci yake.
Mafi ƙarancin albashi albashi a ƙasar yana farawa ne daga kusan PKR 17,500 zuwa PKR 20,000 ($110 zuwa $125) kowane wata.
4. Indiya
Indiya wacce ke a yankin nahiyar Asiya ta shiga cikin jerin ƙasashen da ke da mafi ƙarancin albashi a duniya.
Ma'aikata ba su samun wani albashi mai gwaɓi a ƙasar ta yankin Kudancin Asiya.
Duk da haka, mafi ƙarancin albashi a Indiya kamar a Pakistan ya danganta da jihohi da kuma masana'antu.
Wasu jihohi sun tsayar da mafi ƙarancin albashinsu kan INR 7,000 zuwa INR 9,000 ($95 zuwa $120) kowane wata.
5. Indonesiya
Kamar sauran ƙasashen Asiya, mafi ƙarancin albashi a Indonesiya shi ma ya danganta da yanki.
Mafi ƙarancin albashi a wasu yankunan ƙasar yana kai IDR 3,000,000 zuwa IDR 4,000,000 ($210 zuwa $280) kowane wata.
Jihohin da suka yi ƙarin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jihohin Najeriya guda 12 sun yi wa ma'aikatansu ƙarin albashi.
Jihohin Legas, Ekiti, Oyo, Osun, Ogun, Ondo, Enugu, Ebonyi, Adamawa, Jigawa, Gombe da Katsina na daga cikin jihohi 11 da suka gwangwaje ma'aikatansu da ƙarin albashi.
Asali: Legit.ng