Gwamnatin Tinubu Na Bayar da Tallafin N30,000 Ga 'Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnatin Tinubu Na Bayar da Tallafin N30,000 Ga 'Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu saƙonni da aka yaɗa a WhatsApp da Facebook sun yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya na bayar da tallafin Naira 30,000 ga ɗaukacin ƴan Najeriya
  • A cewar masu yaɗa saƙonnin, ana bayar da tallafin ne domin rage raɗaɗin da ƴan Najeriya suke ciki a halin yanzu
  • Wani dandalin binciken gaskiya ya gudanar da bincike inda ya fitar da sakamakonsa a ranar Laraba, 27 ga watan Maris

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani saƙo da ke yawo a kafar sadarwa ta WhatsApp, ya yi iƙirarin cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu na bayar da tsabar kuɗi N30,000 ga ɗaukacin ƴan Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini a Arewa ya tona manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan bindiga

Gwamnatin Tinubu ba ta raba tallafin N30,000
Batun cewa gwamnatin Tinubu na raba tallafin N30,000 ba gaskiya ba ne Hoto: Kola Sulaimon, Andrew Caballero-Reynolds
Asali: Getty Images

Ana tsadar rayuwa a Najeriya

Matsalar taɓarɓarewar tattalin arziƙin ta kuma janyo zanga-zanga a sassa da dama na ƙasar nan wacce ta fi kowace ƙasa yawan mutane a nahiyar Afirika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Saƙon ya haɗa da wani waje da ake buƙatar a shiga inda aka rubuta "danna nan".

Saƙon na cewa:

“Gwamnatin tarayya ta amince da bayar da tsabar kudi N30,000 ga kowane ɗan Najeriya.
"Dukkan ƴan Najeriya na da damar cin gajiyar wannan tallafin, ku hanzarta yanzu ku duba ku gani ko kun cancanci samun tallafin N30,000 na gwamnatin tarayya. Waɗanda suka nema tuni har an tura musu kuɗin.

An kuma ga irin waɗannan saƙonnin a manhajar Facebook, a nan da nan.

Da gaske gwamnatin Tinubu na bada tallafi?

Amma wannan batun gaskiya ne? Dandalin binciken gaskiya na Africa Check, ya gudanar da bincike a kai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan ayyukan masu garkuwa da mutane, ya gadi matakin dauka a kansu

Dandalin ya ce ya duba sahihan kafafen yaɗa labarai domin ganin ko akwai irin wannan sanarwar, amma bai samu bayanan komai ba dangane da bayar da kuɗaɗe ga ɗaukacin ƴan Najeriya.

Ya yanke hukuncin cewa saƙonnin ana yaɗa su ne domin yaudara da samun mutanen da za su karanta abin da ke ciki.

Tinubu ya ciyo sabon bashin kudi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ciyo bashin ¥15bn.

Gwamnatin ta ciyo bashin nr daga hukumar ƙasa da ƙasa ta Japan domin inganta harkokin noma a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel