Ba a Gama Jimamin Kaduna Ba 'Yan Bindiga Sun Shiga Cikin Jami'a Tare da Yin Awon Gaba da Dalibai
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har cikin harabar jami'ar Calabar (UNICAL) tare da yin awon gaba da wasu ɗalibai
- Rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce an sace ɗaliban ne a wani ɗakin kwanan ɗalibai da ke cikin jami'ar
- Kakakin rundunar ta ce sun yi haɗin gwiwa tare da sauran hukumomin tsaro domin ganin sun kuɓutar da ƴan makarantar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kuros Ribas - Rundunar ƴan sandan jihar Kuros Ribas, a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun sace daliban jami’ar Calabar (UNICAL) guda uku.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Irene Ugbo, ita ce ta tabbatar da sace ɗaliban.
Yadda aka sae ɗaliban
SP Irene ta ce an sace ɗaliban ne a daren ranar Alhamis a ɗaya daga cikin ɗakunan kwanan ɗalibai na jami’ar da ke cikin harabar jami’ar, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ugbo, wacce bata bayar da cikakken bayani game da sace ɗaliban ba, ta ce ƴan sanda na aiki tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro domin ceto ɗaliban.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana sunayen ɗaliban da Ojang Precious Ebejin, Ugwu Chukwuemeka, da Damilola Dickson.
Ƴan bindiga na yawan sace ɗalibai daga makarantu domin samun kuɗin fansa daga iyayensu da gwamnati.
Wasu daga cikin ɗaliban da ƴan bindiga suka sace dai, har yanzu suna tsare a hannun miyagun cikin daji.
Ƴan bindiga sun sace ɗalibai
A baya Legit Hausa ta kawo rahoto cewa wasu ƴan bindigan sun sace wasu ɗaliban wata makarantar Tsangaya a jihar Sokoto.
Ƴan bindigan sun sace ɗaliban ne waɗanda adadinsu ya kai mutum 15 bayan sun yi dirar mikiya a cikin makarantarsu.
An sace ɗalibai a jami'ar FUGUS
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi awon gaba da wasu ɗalibai biyu na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau (FUGUS) a jihsr Zamfara.
Ƴan bindigan sun sace ɗaliban waɗanda namiji da mace ne a ɗakin kwanansu da ke kusa da jami'ar a cikin tsakar dare.
Asali: Legit.ng