An Kashe Wasu Manyan Hatsabiban Ƴan Bindiga 2 da Suka Addabi Bayin Allah a Jihar Arewa

An Kashe Wasu Manyan Hatsabiban Ƴan Bindiga 2 da Suka Addabi Bayin Allah a Jihar Arewa

  • Dakarun ƴan sanda sun samu nasarar kashe hatsabiban ƴan bindiga biyu a ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benuwai
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Cathrine Anene ta ce dakarun sun kama wani ɗan bindiga ɗaya bayan musayar wuta
  • Kwamishinan ƴan sanda ya yabawa jami'an da suka samu wannan nasarar tare da rokon al'umma su ci gaba da taimaka masu da bayanan sirri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai ta kashe wasu manyan hatsabiban ‘yan bindiga guda biyu a karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar.

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar, Cathrine Anene, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba a Makurɗi, Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fitaccen malamin addini a Arewa ya tona manyan mutanen da ke haɗa kai da ƴan bindiga

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Yan sanda sun ga bayan wasu ƴan bindiga a Benuwai Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Anene ta bayyana cewa dakarun ƴan sanda sun kai samame ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ƴan bindiga sun fara taruwa a kauyen De-Mtsa da ke yankin Katsina-Ala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan sandan suka yi nasara

A cewarta, dakarun rundunar Operation Zenda Joint Task Force (JTF) karkashin jagorancin kwamandan su, Felix Nomiyugh, ta yi gaggawar kai samame wurin.

Daga zuwansu suka fara artabu da ƴan bindigar kuma yayin haka ne suka yi nasarar halaka biyu daga cikinsu kuma suka cafko ɗan bindiga ɗaya.

"Daga zuwansu wurin ranar 27 ga watan Maris, ƴan bindigar suka buɗe wa ƴan sandan wuta amma ƙarfin luguden wutar da dakaru suka mayar masu ya tarwatsa su.
"Bayan haka an tabbatar da mutuwar ƴan bindiga biyu da suka ji raunuka a musayar wutar, ƴan sanda sun kana ɗaya yayin da sauran suka tsere ɗauke da raunukan harbi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun shiga daji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Katsina

- Cewar Anene.

Kakakin ƴan sanda ta ƙara da cewa jami'an sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindigar 06, AK47 Magazine guna uku cike da alburusai da wasu harsasai 80 da wayoyi.

CP ya yabawa dakarun ƴan sanda

Sanarwar ta kuma ruwaito kwamishinan ‘yan sandan, Emmanuel Adesina, yana yabawa jami’an bisa jajircewarsu, inda ya roƙi su ci gaba da tunkarar miyagu har maɓoyarsu.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar Benuwai da su rika taimaka wa ‘yan sanda da sahihan bayanai masu amfani kuma a kan lokaci, kamar yadda PM News ta rahoto.

Yan bindiga sun kashe liman a Zamfara

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun halaka Sheikh Ahmad Rufa'i, babban limamin masallacin Juma'a da ke ƙauyen Keita a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Miyagun sun kuma yi awon gaba da mutane masu yawa waɗanda ba a tantance adadinsu ba ciki har da mata a yayin harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel