Duk da Azumin Ramadan da Ake Ciki, an Cafke Malamin Musulunci da Sassan Jikin Ɗan Adam
- Yayin da ake tsaka da gudanar da azumin Ramadan, an cafke wani malamin Musulunci da sassan jikin dan Adam
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama Alfa Oluwafemi Idris a yau Lahadi 31 ga watan Maris a jihar Ondo
- An cafke malamin ne inda ya tabbatar da cewa wani Alhaji da kuma Samuel Kutelu ne suke kawo masa kayan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Rundunar 'yan sanda a jihar Ondo ta cafke wani malamin Musulunci da sassan jikin ɗan Adam.
An cafke Alfa Oluwafemi Idris ne a yankin Akoko da ke jihar da hannayen ɗan adam da hanta da zuciya da harshe da sauransu.
Yadda aka cafke malamin Musulunci a Ondo
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya ita ta tabbatar da haka ne a yau Lahadi 31 ga watan Maris a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Funmilayo ta ce sun yi nasarar cafke malamin ne bayan samun bayanan sirri inda ya ajiye kayan domin yin tsafi.
"Mun gudanar da bincike a gidan malamin inda muka samu hannayen dan Adam da zuciya guda uku da hanta guda uku."
"Sauran kayan da muka samu sun hada da harshen dan Adam da ƙashin bayan mutum."
"Wanda ake zargin ta tabbatar da cewa shi malamin Musulunci ne kuma ya na samun kayan ne daga wani Alhaji da kuma wani mai suna Samuel Kutelu."
- Funmilayo Odunlami-Omisanya
Yan sanda sun bazama neman wadanda ake zargi
An kama sauran mutane biyu da malamin ya ke tura musu kayan domin gudanar da tsaface-tsaface.
Rundunar yanzu haka ta bazama domin cafke daya Alhajin da ake zargin ya na kawo masa sassan jikin ɗan Adam.
Yan bindiga sun sace mutum 2 a coci
A wani labarin, 'yan bindiga sun kutsa kai cikin cocin inda suka sace mambobin cocin guda biyu a jihar Ogun.
Maharan sun ta da hankulan jama'a da harbe-harbe kafin sace matasan guda biyu tare da tserewa da su cikin daji.
Daga bisani rundunar 'yan sanda ta sanar da kubutar daya daga cikin matasan da aka yi garkuwa da su a cocin.
Asali: Legit.ng