Ana Tsaka da Ibada, 'Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Tare da Sace Masu Bauta Guda 2

Ana Tsaka da Ibada, 'Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Tare da Sace Masu Bauta Guda 2

  • Wasu 'yan bindiga sun sake kai farmaki cikin coci inda suka tafka barna a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya
  • Maharan sun kai harin a jiya Alhamis 28 ga watan Maris a kauyen Oriyarin da ke Mowe a jihar yayin da ake cikin bauta
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Omotola Odutola ta tabbatar a yau Juma'a

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - 'Yan bindiga sun kai farmaki wani coci a jihar Ogun inda suka yi garkuwa da mambobin cocin guda biyu.

Maharan sun farmaki cocin Celestial kauyen Oriyarin da ke yankin Mowe a jihar a jiya Alhamis 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shan ruwa, 'yan bindiga sun kai hari, sun sace malamin Musulunci a Arewa

'Yan bindiga sun farmaki wurin ibadarsu tare da sace masu bauta 2
'Yan bindiga sun sace masu bauta 2 a Cocin jihar Ogun. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Twitter

Harin ya firgita mazauna yankin

Harin ya tada hankulan mazauna yankin inda suka firgita yayin da maharan suka yi ta harbe-harbe kafin sace mutanen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da haka a yau Juma'a 29 ga watan Maris, cewar Daily Trust.

Odutola ta tabbatar da hakan ne a birnin Abeokuta inda ta bayyana sunayen wadanda aka sacen da Oladapo Seyifunmi da kuma Oluboboye Abiola.

Ta bayyana cewa maharan bayan sace mambobin cocin sun tsere ta cikin duhun daji da ke yankin.

Matakin da 'yan sanda suka ɗauka

"Rahoton sa muka samu a ranar 28 ga watan Maris ya tabbatar da yin garkuwa da wasu mambobin cocin Celestial guda biyu."
"Maharan sun sace matasan cocin masu suna Oladapo Seyifunmi da Oluboboye Abiola kafin tserewa ta cikin daji."

- Omolola Odutola

Odutola ta ce kwamishinan 'yan sanda a jihar, Abiodun Alamutu ya ba rundunar umarnin ceto wadanda aka sacen ba tare da bata lokaci ba, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai mummunan hari a Yobe, sun hallaka soja

Yan bindiga sun farmaki daliban Jami'a mata

A wani labarin, wasu 'yan bindiga sun farmaki dakin kwanan dalibai mata a Jami'ar Tarayya da ke Lokoa a jihar Kogi.

Maharan sun kai farmaki ne inda duk shafe awanni biyu yayin da suka kwace wayoyi da kudi da sauran kayayyaki masu amfani.

Rundunar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce dalibai biyu sun samu rauni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel