Rikicin Siyasa: Cikin Gwamnan Rivers Ya Duri Ruwa, Majalisa Ta Sake Barazanar Tsige Shi
- Rikicin siyasar jihar Rivers ya sake daukar wani sabon salo yayin da ‘yan majalisar dokokin jihar suka yi gargadin tsige gwamna Sim Fubara
- Majalisar ta Rivers ta yi barazanar tsige Gwamna Fubara ne domin kiyaye kundin tsarin mulkin jihar
- ‘Yan majalisar dai sun zargi Fubara da kin sanya hannu kan wata yarjejeniya, lamarin da ya jawo cece-kuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Port Harcourt, jihar Rivers - ‘Yan majalisar dokokin jihar Rivers sun kuma yin barazanar fara wani sabon shirin tsige gwamna Siminalayi Fubara.
Shugaban majalisar, Martin Amaewhule, ya ce ba zai bata lokaci ba wajen tsige Fubara idan hakan ya zama mataki na karshe na tabbatar da kundin tsarin mulki.
Amaewhule, wanda ke tare da abokan aikinsa 26 ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a Port Harcourt a ranar Asabar, 30 ga Maris, inji rahoton ChannelsTv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda batun ya fara kan rikicin majalisa da Fubara
‘Yan majalisar sun caccaki mambobin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP na jihar karkashin jagorancin Uche Secondus da kuma Dr. Abiye Sekibo kan sukar Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.
Kakakin na majalisar Rivers ya yi zargin cewa Secondus da tawagarsa sun yi aiki da don ganin rashin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Fubara a zaben 2023.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ya ce abin dariya ne ga tawagar ta Secondus ta bayyana goyon bayanta ga Tinubu da Fubara yayin da suke yin shirga kan Wike, wanda ya sa Tinubu da Fubara suka samu nasara.
Dalilin da yasa 'yan majalisar ke son tsige Fubara
A cewar ‘yan majalisar, Gwamna Fubara ya gaza bin yarjejeniyar zaman lafiya da ya sanya wa hannu, kuma ya zabi kin bin wasu sharuddan da aka gindiya.
“Kada su manta cewa Majalisar Dokokin Jihar Rivers ce ke da muryar al’umma kuma mun yi rantsuwar mubaya’a ga Kundin Tsarin Mulki don yin abin da ya kamata ciki har da tsige Gwamna a matsayin matakin karshe.
“Don haka idan har abin ya zama shi ne matakin karshe kamar yadda doka ta tanada, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen yin hakan domin babu wani mutum da ya zarce jihar Rivers har da Gwamna."
Dalilin kulla yarjejeniyar tun farko
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa babu wani farashi wanda za a biya da ya wuce kima domin zaman lafiya a jihar.
Jaridar The Nation ta ce Fubara ya bayyana kudirinsa na tabbatar da zaman lafiya a jihar da tsakanin al’ummarta domin samar da ci gaba.
Wannan alkawarin dai na nuni ne ga yarjejeniyar Abuja, inda shi da sauran masu ruwa da tsaki suka kulla yarjejeniya takwas domin kawo karshen rikicin da ya dade a jihar.
Asali: Legit.ng